Bayern Munich ta nada sabon koci bayan sallamar Nagelsmann

Sabon kocin zai fara jan ragamar kungiyar a ranar Litinin.

Bayern Munich ta nada sabon koci bayan sallamar Nagelsmann

Bayern Munich ta kori kocinta Julian Nagelsmann, bayan kasa da shekaru biyu yana jagorantar kungiyar, inda ta maye gurbin sa da Thomas Tuchel wanda zai ga ragamarta daga nan zuwa 2025.

Tsohon kocin dan asalin kasar Jamus, ya samu nasarar lashe gasar Bundesliga ga kungiyar, inda yanzu haka Munich ta kasance ta biyu a saman teburi, wato maki daya tsakanin ta da Borussia Dortmund, wadda ke mataki na daya.

Bayern Munich dai ta doke Paris St-Germain a Gasar Zakarun Turai, wanda hakan ya bata damar tsallaka wa zagayen dab da na karshe, inda yanzu haka za ta fafata da Manchester City a gasar.

A watan Satumba ne, kungiyar Chelsea da ke buga Firimiyar Ingila ta sallami Tuchel.

Yanzu haka dai, Tuchel ya maye gurbin Nagelsmann wanda ya karbi ragamar kungiyar a watan Yulin 2021, kuma kwantaragin sa zai kare ne a ranar 30 ga watan Yunin 2025.

Bayern Munich ta ce, sabon kocin zai fara jan ragamar kungiyar ne a ranar Litinin.

Haka zalika Munich, ta kuma tabbatar da cewa, masu taimaka wa kocin, Dino Toppmoller, Benjamin Gluck da kuma Xaver Zembrod sun bar kungiyar.