Bayern Munich za ta kece raini da Real Madrid a kofin Audi
Ana sa ran kulob din Real Madrid na Sifen yana daga cikin kulob hudu da kulob din Bayern Munich na Jamus ya gayyato wadanda za su fafata a gasar cin kofin Audi a bana. Ana gudanar da gasar ce a duk bayan shekara biyu. Sai dai a makon farko a watan gobe ne ake sa […]
Ana sa ran kulob din Real Madrid na Sifen yana daga cikin kulob hudu da kulob din Bayern Munich na Jamus ya gayyato wadanda za su fafata a gasar cin kofin Audi a bana. Ana gudanar da gasar ce a duk bayan shekara biyu.
Sai dai a makon farko a watan gobe ne ake sa ran Bayern Munich zai bayar da sanarwar sauran kulob biyun da suka rage.wadanda za su fafata a gasar.
A ranar 4 da kuma 5 ga watan Agusta mai zuwa ne ake sa ran gasar za ta gudana.
A gasar da Munich ta shirya a shekarar 2013, kulob din na Munich ya fafata ne da na Manchester City daga Ingila da na AC Milan daga Italiya da kuma na Sao Polo daga Brazil.
Kamfanin kera motoci na Audi ne yake daukar nauyin gasar, kuma ana gudanar da ita ne duk bayan shekara biyu a filin wasa na Munich da ake kira Allianz Arena.
Wannan gasa ta cin kofin Audi takan ba kungiyoyin kwallon kafa damar yin shiri don tunkarar sabuwar kakar wasa.