bayyade mu’amalar kafafen sadarwar zamani a basashen duniya (I)
Mabudi: Yunburin da Majalisar Dattawa ta basa ke yi a yanzu don amincewa da budirin da Sanata Bala Ibn Na’Allah ya gabatar mata mai taken: “Bill for an Act to Prohibit Fribolous Petitions and Other Matters Connected Therewith,” wato: “budiri Don Samar da Dokar Hana borafi da Zargi Mara Tushe da Makamantansu,” abu ne da […]
Mabudi:
Yunburin da Majalisar Dattawa ta basa ke yi a yanzu don amincewa da budirin da Sanata Bala Ibn Na’Allah ya gabatar mata mai taken: “Bill for an Act to Prohibit Fribolous Petitions and Other Matters Connected Therewith,” wato: “budiri Don Samar da Dokar Hana borafi da Zargi Mara Tushe da Makamantansu,” abu ne da ke kan tayar da bura a tsakanin jama’ar basa. Wannan budiri, idan har ya zama doka ta basa, zai zama dokar farko da aka taba yi a Najeriya wajen bayyade fadin albarkacin baki a kafafen sadarwa, musamman na zamani. Wannan budiri dai a halin yanzu an yi nazarinsa har sau biyu, sauran nazarin barshe.
Masana nakan tattaunawa a kan fa’ida da kuma matsalolin da suke ganin samar da wannan doka zai haifar. Masu goyon baya na ganin za ta rage yawan zargi mara tushe da kafafen watsa labarai ta hanyar Intanet suke yi ga shugabannin siyasa da ma’aikatan gwamnati. Sannan za ta zama wata hanya ta farko da gwamnati za ta bi wajen koya wa al’umma tarbiyyar zance da rubutu a kafafen sadarwa na zamani, musamman dandalin abota irin su: Twitter, da Facebook da Imel da Youtube da sauransu. Masu wannan ra’ayi suka ce babu wata basa a duniya da ba ta da wata doka da ke bayyade mu’amalar al’ummarta a wannan sabuwar duniya ta sadarwa. Masu adawa da wannan budiri kuma, wadanda galibinsu ’yan jarida ne da sauran al’ummar basa, suka ce wannan wani yunburi ne na kame bakin al’umma da hana su fadin albarkacin bakinsu. Suka bara cewa, masu goyon bayan wannan budiri musamman a majalisa suna bobarin boye badabalar da suke yi ne a barbashin basa, ta hanyar amfani da dokar basa.
Wannan budiri har wa yau, ya hada da sabonnin tes na wayar salula da sabonnin Imel da na jaridun Intanet ko na zahiri da na talabijin da na rediyo – na Intanet ko na zahiri. Kowannensu ana iya karba da amincewa da shi a kotu, a matsayin shaida kan mutumin da ya zargi wani ba tare da hujja bwabbwara ba. Idan ba a manta ba, akwai budirin da aka taba gabatar wa majalisar da ta gabata kan amincewa da sabonnin tes da na Imel a matsayin shaida a kotu. Amma har majalisar ta kwashe shekarunta, ba a barbare batun ba. Ta yiwu wannan buduri ya maye gurbin wancan, domin ga dukkan alamu, sawun giwa na bobarin take na rabumi.
Idan ba a mance ba dai, cikin shekarun da suka gabata ne sauran basashen duniya, musamman ma Turai da Amurka suka kafa wa basar Sin bahon-zuba da azalzala, cewa, ta taka dokar dan Adam, sanadiyyar sabuwar dokar da ta fitar, cewa, duk wata kwamfuta da za ta shiga basar a matsayin kayan sayarwa ko amfani, dole ne kamfani ko dillalin da zai shigo da ita ya sanya mata wata manhajar tacewa da ta tanada mai suna Green Dam Youth Escort.
Wannan masarrafa ta kwamfuta aikinta, shi ne, lura da gidajen yanar sadarwar da mai amfani da kwamfutar ke ziyarta da kuma tabbatar da cewa, ta hana shi shiga wasu gidajen yanar sadarwa na batsa, kamar yadda Hukumar Sadarwar basar ta sanar. Wannan, inji gwamnati, shi ne, dalilin bullo da wannan sabuwar doka. Kuma tuni hukuma ta fara aiki kafada-da-kafada da kamfanonin shigo da kwamfuta basar, irin su Apple, da Microsoft Inc da sauransu, don ganin sun fara shigar da wannan sabuwar manhaja ko masarrafa cikin dukkan kwamfutocin da za su shigar da su basar don sayarwa ko aiki da su nan gaba.
Sai dai kuma yana da muhimmanci mai karatu ya fahimci cewa, wannan laifi da ake zargin basar Sin a kansa, akwai basashe sama da 50 – ciki har da basar Amurka da Birtaniya da Faransa da Jamus da Rasha da Isra’ila- da tuni sun yi baurin suna a hukumance wajen kare irin nau’in bayanan da ke Intanet, ta hanyoyi daban-daban. In kuwa haka ne, wannan ke nuna lallai akwai wata matsala ke nan gamammiya dangane da tasirin wannan fasaha.
Don me basashe ke bobarin bayyade tsarin mu’amala da kafafen sadarwa na zamani? Wasu hanyoyi ake bi wajen yin wannan aiki? Wai shin, zai ma yiwu a sanya wa wannan fasaha takunkumi har hakan ya yi tasiri? Wadannan da wasu tambayoyi masu muhimmanci ne wannan basida za ta yi bobarin amsawa cikin wannan silsila mai matubar muhimmanci. Hakan zai ba mu damar fahimtar muhimmanci ko rashin muhimmancin wannan buduri da ke gaban Majalisar Dattawa a halin yanzu, a tarihance, da fasahance. Da farko za mu fara da dalilan da ke sa basashe ke daukar wannan mataki.
Don me ake bayyade tsarin mu’amala da Intanet?
A tabaice, tsarin hana shigar da wasu bayanai na musamman cikin Intanet, ko bayyade yanayin samunsu ga jama’ar wata basa ko al’umma, ko kuma hana mu’amala da wannan fasaha ta Intanet yadda mai yin hakan ke so, ko toshe ba’idar da ke sadar da shi ko wani gidan yanar sadarwa na musamman, ko amfani da doka wajen bayyade tsarin mu’amala, shi ake nufi da sanya wa fasahar Intanet takunkumi, wato “Internet Censorship” ke nan, a Turancin kwamfuta. Wannan aiki kuwa ba wani ba ne ke yi illa gwamnatocin basashe ko hukumomin da ke wakiltarsu. Amma takunkumin da wasu ke sanyawa a gidajen yanar sadarwarsu, ta yadda ba ka iya ganin wasu bayanai ko samunsu, musamman a gidajen yanar sadarwar kasuwanci ko wasu harkokin kudi, ba a kiransa da Internet Censorship. Amma wanda basashe ke yi yana shafar hatta asalin fasahar ce, kamar yadda mai karatu zai karanta nan gaba.