Bayyana kadarori: Koyi da Buhari ba dole ba ne – Gwamna Lalong
A makon jiya ne Gwamnan Jihar Filato Barista Simon Lalong ya tattauna da ’yan jarida kan cika kwana 100 a kujerar Gwamnan, inda ya bayyana cewa ba dole ni gwamnoni su yi koyi da Buhari wajen bayyana dukiyar da suka mallaka ba. Kuma ya yi zargin cewa jami’an tsohon Gwamnan Jihar Jonah Jang sun takfa […]
A makon jiya ne Gwamnan Jihar Filato Barista Simon Lalong ya tattauna da ’yan jarida kan cika kwana 100 a kujerar Gwamnan, inda ya bayyana cewa ba dole ni gwamnoni su yi koyi da Buhari wajen bayyana dukiyar da suka mallaka ba. Kuma ya yi zargin cewa jami’an tsohon Gwamnan Jihar Jonah Jang sun takfa mummunar sata, shi ya sa suka mika sunayen wadanda ake zargi ga Hukumar EFCC don gudanar da bincike:
Aminiya: Lokacin da ka karbi rahoton kwamitin binciken gwamnatin da ta gabata, ka ce wadanda suka wawushe kudin jihar su dawo da su a cikin mako biyu ko ku mika su ga Hukumar EFCC. Wane hali ake ciki kan al’amarin?
Gwamna Lalong: Dangane da umarnin da muka bai wa wadanda suka wawushe kudin jihar nan a zamanin gwamnatin da ta gabata, cewa su dawo da kudin cikin mako biyu ko mu mika su ga Hukumar EFCC, na bayar da mako biyu amma ana ganin abin kamar wasa ne. Ganin yadda mutane suka yi biris da wannan umarni da muka bayar, sai muka tura sunayen mutanen ga Hukumar EFCC. Jami’an Hukumar EFCC suna shirin binciken mutanen game da kudin Jihar Filato da suka wawushe. Bayan haka akwai wasu kamfanoni biyu da su ma za su zo su yi mana bincike a kan wannan al’amari. Mutanen sun yi mummunar satar kudin al’ummar Jihar Filato, a cikinsu akwai mutum daya da ya sace albashin ma’aikatan kananan hukumomin jihar na wata biyu. Mun gano cewa an biya kudin a asusun ajiyar mutumin wanda jami’in gwamnatin da ta gabata ne. Kuma ina kara fadi har yanzu idan har da wanda yake rike da kudin al’ummar Filato, in ba ya son ya gurfana a gaban Hukumar EFCC ya dawo da kudin. Mutanen Filato ba za su yarda mutum biyu su wawushe kudin al’ummar Filato har Naira biliyan 200 su tafi haka kawai ba.
Aminiya: Wane hali ake ciki game da tallafin da Gwamnatin Tarayya ta ba ku don biyan bashin albashin ma’aikata?
Gwamna Lalong: Gaskiyar magana har zuwa wannan lokaci a Jihar Filato ba mu karbi wannan tallafi da Gwamnatin Tarayya ta bai wa jihohi ba. Na karanta a jaridu cewa wai mun karbi kudin, gaskiyar magana har zuwa wannan lokaci Jihar Filato ba ta karbi kudin ba. Duk nasarorin da muka samu a kwana 100 da muka yi a mulkin jihar, mun same su ne ba da tallafin kudin ba. Kuma daga hawanmu mulki zuwa yanzu mun karbo bashin Naira biliyan hudu da rabi ne kawai. Da wannan kudi ne muka biya albashin ma’aikata na wata shida. Muna sa ran nan da mako biyu za mu samu wannan tallafi na Gwamnatin Tarayya, inda za mu ci gaba da biyan sauran bashin albashin da ma’aikata suke bi.
Aminiya: Ganin yadda rikici a yankin Barikin Ladi, ya ki ci ya ki cinyewa, wadanne matakai ne gwamnatinka take dauka don magance lamarin?
Gwamna Lalong: Wannan rikici na yankin Barikin Ladi babban abin takaici ne a gare mu, domin a wannan rikici ne za ka ga an kone dukiyar mutane baki daya, wani bangaren ka ga an karkashe shanun al’umma. Daga lokacin da muka karbi mulki zuwa yanzu, mun yi iyakar kokarinmu wajen ganin mun kawo karshen rikicin na yankin Barikin Ladi. Na zauna da Mai girma Shugaban kasa har sau biyar kan rikicin yankin Barikin Ladi, kuma na tabbatar masa cewa zan yi iyakar kokarina wajen ganin na magance rikicin. Bayan haka, mun nemi Gwamnatin Tarayya ta kara mana jami’an tsaro zuwa yankin, kuma ta amshi rokon namu ta turo mana karin jami’an tsaro sama da 150. Gwamnatin Jihar Filato ce take daukar nauyin biyan duk alawus-alawus din jami’an tsaron. Har ila yau mun kafa kwamitin sasanta wannan rikici, inda muka debi mutum bakwai daga kabilar Berom da bakwai daga al’ummar Fulani, sai gwamnatin jiha ta samar da shugaba da sakataren kwamitin, muka ba su aiki su zauna su tattauna hanyoyin da za a bi a warware wannan matsala. A nan ina sake mika rokonmu ga Shugaban kasa, a tallafa mana kan wannan rikici na Barikin Ladi, kamar yadda Gwamnatin Tarayya take tallafa wa jihohin Arewa maso Gabas da suke fama da rikicin Bako Haram. Idan aka tallafa mana da kudi za mu yi amfani da su don tallafa wa al’ummomin da rikicin ya shafa, wajen sake gina musu gidajen da aka kone da biyan diyya ga masu dabobin da aka karkashe ko aka sace. Domin Gwamnatin Jihar Filato ba za ta iya daukar nauyin wannan lamari ita kadai ba, saboda dimbin basussukan da ta gada.
Aminiya: Mutane suna ta maganganu kan yadda har zuwa wannan lokaci ba ka bayyana sunayen kwamishinoni da masu taimaka maka ba, me za ka ce?
Gwamna Lalong: Dangane da rashin bayyana sunayen kwamishinoni da masu taimaka mini, gaskiya mun gaji dimbin basussukan albashin ma’aikata, don haka ba ma son mu kara wa kanmu nauyi cikin gaggawa. Ya kamata jama’a su fahimci cewa har yanzu ba mu gama biyan bashin albashin da ma’aikatan jiha suke bi ba. Tunda na hau mulkin jihar nan, har yanzu ban taba karbar albashi ba. Don haka ina kira ga ’yan siyasar da muke tare su kara hakuri mu biya ma’aikata bashin albashin da suke bi tukuna. Idan muka gama biya daga nan sai su san abin da za mu yi.
Aminiya: A kwanaki Shugaban kasa Buhari ya bayyana yawan dukiyar da ya mallaka kafin ya hau mulki. Ko kai ma za ka bayyana wa duniya yawan dukiyar da ka mallaka?
Gwamna Lalong: To, game da bayyana dukiyar da na mallaka kafin na hau mulkin jihar nan, ai tuni mun bayyana dukiyar da muka mallaka ga Hukumar da’ar Ma’aikata ta kasa, a takardar da muka cike lokacin da muka shiga takara. A dokar tsayawa takarar zabe ba a ce dole sai mutum ya bayyana wa duniya yawan dukiyar da ya mallaka ba. Wannan ya rage ga Hukumar da’ar Ma’aikatan ta bayyana wa duniya dukiyar da muka mallaka, amma doka ba ta ce mu bayyana da kanmu ba. Mu dai abin da doka ta ce shi ne mu bayyana wa hukumar kadai shi ne dokar ta ce. Idan doka ta ce mu bayyana sai mu bayyana, don mara wa shirin Shugaban kasa baya kan yaki da cin hanci a kasar nan.