Bayyana kadarorin da Buhari da mataimakinsa suka yi ga hukuma ya wadatar ko su bayyana wa al’umma?
A kwanakin baya ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yomi Osinbajo suka gabatar da bayanin kadarorin da suka mallaka ga Hukumar Kiyaye da’ar Ma’aikata, kamar yadda Tsarin Mulkin kasa ya tanadar. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko hakan da suka yi ya wadatar ko kuwa ya kamata su bayyana kadarorin nasu a […]
A kwanakin baya ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yomi Osinbajo suka gabatar da bayanin kadarorin da suka mallaka ga Hukumar Kiyaye da’ar Ma’aikata, kamar yadda Tsarin Mulkin kasa ya tanadar. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko hakan da suka yi ya wadatar ko kuwa ya kamata su bayyana kadarorin nasu a bainar jama’a? Aminiya ta kalato ra’ayoyin jama’a kan wannan, kamar haka:
Bayyana kadarorin ga hukuma ya wadatar – Ala Katsina
Ahmad Kabir, a Katsina
Alhaji Ala Katsina: “Bai dace a ce Buhari da Mataimakinsa su bayyana abin da suka mallaka ga jama’a ba, tun da sun riga sun bayyana wa hukumar da abin ya shafa. Dalili shi ne, inda ba su da gaskiya ai da ba su cika wannan doka ba. Amma saboda gaskiya da amanarsu ya sa har jama’ar Najeriya suka yarda da su kuma muka ba su amanar kasar. Kuma Buhari mutun ne wanda aka sani maras munafunci, don haka mun tabbatar da duk abin da suka bayyana wa wannan hukuma gaskiya ne ba zai yi karya ba kuma shi mutun ne mai son tsare doka. In kuwa da ba haka dokar ta tanada ba da ba zai yi haka ba sai ya bi yadda doka ta ce. A takaice, bai kamata su bayyana wa jama’a ba.”
Su bayyana a bainar jama’a ya fi – Hafsat Suleiman
Ahmad Kabir, a Katsina
Hafsat M. Suleiman: “Ya kamata su bayyana wa jama’a, ba ga hukumar ita kadai ba kuma a asirce. Dalili shi ne, wannan zai sa su ma na baya su bayyana nasu yadda kowa zai sani. Amma barin abin a asirce zai sa jama’a su rika wasiwasi duk kuwa da an san cewa mutun ne mai gaskiya kuma mai kokarin ganin an tsaya wa gaskiyar. Amma yin hakan daga wajensa zai sa sauran wadanda za su shugabance mu tilas su yi haka. An yi maganin zamba ke nan.”
Bayyanawa ga jama’a zai zama abin koyi – Muhammad Yahaya
Abubakar Haruna, a Legas
Dokta Muhammad Yahaya: “Ya kamata Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Mataimakinsa Osinbajo su bayyana wa ’yan Najeriya kadarorinsu saboda ya zama darasi da abin koyi ga shugabannin da za su zo nan gaba. Ka ga ke nan idan wasu shugabannin suka shigo, dole su ma su bayyana nasu kadarorin ba tare da wata matsala ba.”
Hakan zai kare su daga zargi – Jibo danyaro
Abubakar Haruna, a Legas
Jibo danyaro Wanzam: “A ganina, ya dace Shugaba Muhammadu Buhari da Osinbajo su fito fili su bayyana kadarorinsu ga ’yan Najeriya saboda hakan shi zai kare su daga dukkan zarge-zargen aikata laifin almundahana da cin hanci da rashawa bayan sun sauka daga kan mulki. Saboda idan aka duba aka tabbatar cewa dukiyoyinsu ba su karu fiye da yadda doka ta tanada ba, babu wanda zai zarge su.”
Lallai ya dace su bayyana a fili – Tukur Ibrahim
Shu’aibu Ibrahim, a Gusau
Tukur Ibrahim: “Ni ra’ayina, Shugaban kasa da mataimakinsa ya dace su bayyana kadarorinsu a fili kowa ya sani ba a boye ba, haka kuma idan suka sauka domin a halin da ake ciki yanzu da suka bayyana kadarorinsu ba kowa ya san adadin abin da suka mallaka ba, musamman kuma a ce sauran ’yan Najeriya kauyawa irinmu. Ya dace su san matsayin wanda suka zaba da abin da ya mallaka amma idan ba haka suka yi ba, to sun bar masoyansu cikin duhu, koda sun sauka suka bayyana zai zama babu amfani.”
Bai dace su bayyana a fili ba- Mika’ilu Sani
Shu’aibu Ibrahim, a Gusau
Mika’ilu Sani: “A ra’ayina, bai dace Shugaban kasa da mataimakinsa su bayyana kadarorinsu a fili ba saboda ai dama amfanin wannan hukumar ke nan, su ba da takardu a cike. Ba ya cikin ka’idojinsu cewa duk wanda zai bayyana kadararsa ya shiga rediyo ya bayyana wa duniya kowa ya sani. Da akwai bukatar haka da ita hukumar ta samar da hurumin yin haka tun tuni, ba sai yanzu ba, don haka yadda suka bayar shi ke nana ya wadatar sai kuma bayan sun sauka sai su sake cikewa, idan ana so a kama su da laifi sai a bincike su bayan saukar su. Abin da bincike ya nuna shi ne zai samar da matsayinsu.”