Bayyanar Sheikh Inyass a gilashin masallaci ba gaskiya ba ne – Sheikh Tafoki
daya daga cikin manyan malaman darika a Kaduna, Malam Mustapha Abdullahi Tafoki ya musanta zancen da ake yayatawa cewa Sheikh Ibrahim Nyass ya bayyana a gilashin Masallacin Juma’a na Tudun Wada, Kaduna inda Shekih dahiru Usman Bauchi yake gudanar da tafsiri a watan azumin Ramadan.Sheikh Mustapha Tafoki ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa […]

daya daga cikin manyan malaman darika a Kaduna, Malam Mustapha Abdullahi Tafoki ya musanta zancen da ake yayatawa cewa Sheikh Ibrahim Nyass ya bayyana a gilashin Masallacin Juma’a na Tudun Wada, Kaduna inda Shekih dahiru Usman Bauchi yake gudanar da tafsiri a watan azumin Ramadan.
Sheikh Mustapha Tafoki ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu a daidai lokacin da daruruwan jama’a ke tururuwa zuwa masallacin domin ganin Sheikh Nyass da aka ce ya bayyana a gilashin masallacin a ranar Juma’ar da ta gabata.
Ya ce “A ra’ayina Allah Yana iya yin komai yadda Ya so, amma maganar a nan ita ce idan ma ya fito sai me? Ka yi magana da shi ne ko ya yi magana da mutane ne? Na samu labarin wasu ma sun je wurin suna yin sujada da rokon ya taimake su. Duk wanda ya je wurin ya yi sujada to, ya yi shirka saboda haka ba gaskiya ba ne. A ra’ayina bayyanarsa ko rashin bayyanarsa ba matsalata ba ce. Domin koda na je wurin ni ma ban ga komai ba. Kuma wasu sun ce wai a gilashi ya bayyana. To, a canja gilashin mana a ga ko zai bayyana. Wadanda ba sa yawo a duniya su ne abin zai ba su mamaki.”
Malamin wanda ya nuna bacin ransa ya kuma nanata cewa dole ne matasa su tashi tsaye su yi karatu su kuma rika bin Sunnar Manzon Allah (SAW).
“Muna sane da cewa akwai mutanen da suka yi karatu amma sai suka fake da sunan Inyass suna bokanci duk wannan bai dace ba. Sannan akwai masu son yin koyi da kyawawan halayensa,” inji shi.
Malam Tafoki ya ce a yau da Manzon Allah (SAW) zai dawo duniya sai ya ce wasu ba Musulunci suke yi ba, haka ma da Shehu Tijjani zai dawo zai ce da yawa ba addinin ake yi ba.
“Wannan ya sa muke jawo hankulan ’yan uwa Musulmi musamman a wuraren maulidi da wa’azozinmu cewa su tashi su yi karatu wadanda kuma suke da karatu su ci gaba da neman ilimi saboda kauce wa aikata shirka,”inji shi.
A cewarsa, a duk lokacin da suka ga mutane na neman kaucewa daga tsarin Musulunci na gaskiya ba sa shiru sai sun yi magana a kai, kamar yadda suka yi Allah wadai da wanda ya yi wakar da ta nemi ba Shehu Nyass matsayin Allah.
“In ban da Allah babu wanda ake yi masa sujada a nemi taimako. Saboda haka Sheikh Ibrahim mutum ne kuma mutumin kirki. Waliyi ne shi, amma bai kai matsayin sahabi ba. Mutane su lura cewa imani shi ke wa mutum jagoranci a matsayinsa na Musulmi. Don haka komai za a nema a nema a wurin Allah,” inji shi.
Malamin ya yi kira ga Musulmi su yi ta karatu kuma in za su yi karatu su san wurin malamin da za su je neman karatu.
A ranar Asabar da Lahadin da suka gabata daruruwan jama’a sun yi ta tururuwa zuwa Masallacin Sheikh dahiru Bauchi domin ganin hoton Sheikh Nyass da aka ce ya bayyana a gilashin masallacin a ranar Juma’a. Mutane masu yawa daga unguwanni sun yi ta tururuwa zuwa masallacin don ganin hoton malamin wanda ya rasu shekaru masu yawa da suka wuce.
Aminiya ta jiyo cewa kusan karfe 3:00 na yammacin ranar ce daya daga cikin masallatan ya ce ya ga hoton Inyass ya bayyana a jikin bangon masallacin. Lokacin da wakilinmu ya ziyarci masallacin ya tarar da matasa da ’yan mata da matan aure da tsofaffi sun taru suna ta kallon bangon, wasu na cewa sun gan shi wasu na cewa ba su ga komai ba.
Akilu Zubairu daya daga cikin matasan da suka je wurin ya ce “Gaskiya ni ban ga komai ba da na je kuma ina masallacin tun kusan karfe 10 na dare har karfe daya na dare. Saboda na ce ban gan shi ba sai wasu ke cewa wai ni dan wuta ne in je in yi ta istigifari.”
Wani matashi da ya ki fadin sunansa cewa ya yi. “Ni dai na gan shi ya daga hannunsa kamar yana addu’a. Kuma na ji dadi a raina. Sai dai hotonsa bai fito sosai ba kamar yadda ya fito a Jihar Nasarawa.”
Wani dan acaba da bai fadi sunansa ba ya shaida wa Aminiya cewa “Ni dan darika ne sosai, amma ban ga dalilin da mutane suke daukar ganin Inyass a matsayin wani abu na ban mamaki ba. Ina mamakin a ce wai mutum ya mutu shekaru masu yawa amma a ce wai yana bayyana mutane su gan shi. Sai dai duk abin da za ka fada wa mutane ba za su yarda ba, saboda son da suke yi masa. Shi ya sa za ka ga suna ta cewa sun gan shi, amma gaskiya ni ban ga komai ba sai jirwayen ruwa a gilashin masallacin.”
Wata majiya ta ce daga baya an tura ’yan sanda masallacin inda suka tarwatsa mutanen da ke zuwa kallon.