Bazamfariya ta yi tsintuwar kusan Naira miliyan 60 a Saudiyya

Wata Hajiyar Najeriya ’yar asalin Jihar Zamfara, Aishatu ’yan Guru Nahuce, ta yi tsintuwar dala 80,000 a Saudiyya kuma ta nemi mamallakin kudin ta mayar. Maruwaita rahotannin Aikin Hajjin ne suka sanar da hakan cikin wani sako da suka wallafa a ranar Asabar a shafinsu na Facebook. Yadda tsananin zafi ya sa Alhazai Sallah a […]

Bazamfariya ta yi tsintuwar kusan Naira miliyan 60 a Saudiyya

Wata Hajiyar Najeriya ’yar asalin Jihar Zamfara, Aishatu ’yan Guru Nahuce, ta yi tsintuwar dala 80,000 a Saudiyya kuma ta nemi mamallakin kudin ta mayar.

Maruwaita rahotannin Aikin Hajjin ne suka sanar da hakan cikin wani sako da suka wallafa a ranar Asabar a shafinsu na Facebook.

Haka kuma, sun wallafa hoton Hajiyar wadda ta fito daga Karamar Hukumar Bungudu ta Jihar Zamfara.

A cewar sakon, “wannan Hajiyar Najeriya ce mai suna Aishatu ’yan Guru Nahuce da ta fito daga Karamar Hukumar Bungudu ta Jihar Zamfara.

“Ta tsinci $80,000 (kimamin N56,000,000) kuma ta mika wa Hukumar Kula da Walwalar Alhazai ta Jihar Zamfara domin a mayar wa wanda ya jefar da kudin.

“Muna rokon Allah Ya ba ta ladan wannan gaskiya da ta yi kuma Ya sa Aikin Hajjin da ta yi ya zama karbabbe

Tuni dai mabiya dandalin sada zumunta na Facebook suka rika bayyana ra’ayoyi mabanbanta dangane da wannan abun a yaba da matar ta yi.

A yayin da an samu masu yabawa da wannan kai zuciya nesa da ta yi, wasu kuma sun jefa ayar tambaya kan mai wani mahaluki zai yi da zunzurutun kudi har dala 80,000?

A bana dai, akalla maniyyatan Najeriya 95,000 ne suka sauke farali a yayin Aikin Hajjin na bana.

DAGA LARABA: Yadda Almajiri Ya Zama Mabaraci

Tinubu ya dawo Abuja bayan halartar taro a Saudiyya

Zaɓen Ondo: Atiku ya gargaɗi INEC kan tafka maguɗin zaɓe

Sojoji sun tafka ƙazamin artabu da Bello Turji a Sakkwato