Bazaranar tsaro: An rufe Kasuwar Mammy da ke Damaturu
Hare-haren bom sun yawaita a wuraren sharholiya a kwanan nan
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Yobe ta rufe Kasuwar Mammy da ke gab da Ofishin Babban Jami’in ’Yan Sandan Yanki da ke garin Damaturu, hedikwatar jihar, saboda fargabar hare-haren ’yan ta’adda.
Rundunar ta dauki matakin ne bayan hare-haren bom na kwanan na da ’yan ta’adda suka kai yawaitar kaiwa a mashaya da sauran wuraren sharholiya.
- NAJERIYA A YAU: Za A Kai Wa Wuraren Ibada Harin Bom —DSS
- Aisha Buhari ta yada bidiyon zargin sojoji da taimakon ’yan bindigar Zamfara
Jami’in Hulda da Jama’a na rundunar, ASP Dungus Abdulkarim, ya ce an dauki matakin ne domin gudun kada ’yan ta’adda su shammace su, sakamakon “Abin da ya faru a Geidam da Gashua.
“Yana da kyau a gare mu mu yi taka-tsantsan ta hanyar rufe Kasuwar Mammy ta Area Command har sai abin da hali ya yi.”
A cewarsa, rundunar tana hada kai da sauran hukumomin tsaro da ke aiki a jihar domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta fitar da sanarwar ankarar da jama’a game yiwuwar hare-haren bom a cikin.
Hukumar ta ce ta bankado shirye-shiryen da wasu masu aikata laifi na mayar da Najeriya tamkar a zamanin da ake ciki kafin shekarar 2015 wajen kai hare-haren bom a wurare taurwar jam’a.
Hukumar ta bakin kakakinta, Peter Afunanya, ta shawarci masu wuraren taruwar jama’a da masu gudanar da wuraren da su yi hattara tare da aiwatar da matakan tsaro na yau da kullum domin dakile barazanar da wadannan mugayen mutane ke shiryawa.