Bazawara ta auri karenta a Birtaniya
Wata mata mai kimanin shekara 46, ’yar asalin Birtaniya mai suna Amanda Rodgers ta auri karenta da ake kira Sheba, bayan ta rabu da mijinta da suka kwashe kimanin shekara 20 tare.Amanda ta ce bayan ta rabu da mijinta da suka kwashe tsawon lokaci suna tare ne, sai ta ji babu wanda ya kwanta mata […]
Wata mata mai kimanin shekara 46, ’yar asalin Birtaniya mai suna Amanda Rodgers ta auri karenta da ake kira Sheba, bayan ta rabu da mijinta da suka kwashe kimanin shekara 20 tare.
Amanda ta ce bayan ta rabu da mijinta da suka kwashe tsawon lokaci suna tare ne, sai ta ji babu wanda ya kwanta mata a rai, a matsayin wanda take son aura da ya wuce karenta Sheba.
Rahoton da kafar sadarwar naij.com ta kalato, ya nuna saboda murnar bikinta da kare Sheba ne ya sa ta gayyato manyan baki kimanin 200. Sannan daruruwan ’yan kallo sun halarci bikin daurin auren.
Rahoton ya ce a lokacin daura auren, Amanda ta sanya bakaken kaya ne da ke sheki a matsayin amarya yayin da shi kuma kare Sheba aka kawata shi da fararen kaya a matsayinsa na ango.
Jim kadan da daura auren nasu ne, sai Amanda ta bayyana cewa ta shafe lokaci mai tsawo tana tare da karenta Sheba kuma a mafi yawan lokuta yakan debe mata kewa ta hanyar ba ta dariya da kwantar mata da hankali, don haka ta yanke shawarar babu wanda ya cancanci ta aura da ya wuce shi.
Tuni amarya Amanda ta tare a dakinta da kare Sheba.