Bazawara ta kashe kanta kan zargin tsangwama a gidan iyaye
Wata uwar ’ya’ya biyu da ke tare da iyayenta bayan mutuwar aurenta, ta kashe kanta bayan ta yi zargin tsangwama daga wajen magabatanta a gidan iyayenta. Matar mai suna A’isha Umaru, bayanai sun ce ta sha gubar kwari da ta sayo da kanta ne a unguwarsu ta Malam Shehu da ke Garin Suleja a Jihar […]
Marigayiyar A’isha Umaru da ake zargin da kashe kanta
Wata uwar ’ya’ya biyu da ke tare da iyayenta bayan mutuwar aurenta, ta kashe kanta bayan ta yi zargin tsangwama daga wajen magabatanta a gidan iyayenta.
Matar mai suna A’isha Umaru, bayanai sun ce ta sha gubar kwari da ta sayo da kanta ne a unguwarsu ta Malam Shehu da ke Garin Suleja a Jihar Neja.
Wani dan uwan marigayiyar da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa wakilinmu cewa lamarin wanda ya faru a ranar Lahadin makon jiya, ya faru ne bayan kwanaki kadan da ’yan sanda suka kamata a kan wata babbar waya da ta saya wadda aka gano ta sata ce. Ya ce hakan ya sa iyayenta suka yi mata fada. Ya ce ’yar uwar tasa, wacce take harkar sayar da atamfa baya ga shiga al’amuran siyasa, ta gamu da rigimar wayar ce bayan wani makwabcinsu ya sayar mata da ita a kan Naira dubu 25.
“Ba a fi kwana biyu da yin haka ba, sai ’yan sanda suka zo unguwarmu suka kamata, bayan sun yi amfani da na’ura wajen gano inda wayar take. Sun tafi da ita zuwa ofishinsu da ke Kaduna Road inda ainihin masu wayar suka shigar da kara, kuma bayan ta yi wa ’yan sanda bayanin wajen wanda ta sayi wayar, sai ’yan sanda suka gayyace shi, sannan aka sake ta.
Sai dai daga baya shi ma an bada belinsa bayan ya sanar da su wajen wanda ya sayi wayar.
Dan uwan marigayiyar ya ce daga baya iyayenta sun ja kunnenta a kan ta rika taka-tsantsan da al’amura. “To bayan gari ya waye a ranar Lahadi, sai ta fita daga gida ta je ta sayo maganin kwari ta shiga daki, ta kurbi kadan kamar yadda muka gano.
“Tana tare da wadansu kannenta ’yan mata biyu a dakin, yayin da ’yan’yanta biyu kuma daya ke wajen mahaifinsa wato tsohon mijinta, dayar kuma ke kwana a dakin mahaifiyarmu da ke gidanmu. Bayan ta sha sai ta tayar da daya daga cikin ’yan matan mai suna Hauwa, ta sanar da ita cewa ta sha guba. Dama ta jima tana cewa ita za ta kashe kanta kowa ya huta, amma ba wanda ya taba tsammanin da gaske take yi,” inji shi.
“Yarinyar ta yi ta yi mata fada lokacin, sannan ta hanzarta sanar da mahaifiyarmu. An dura mata manja a baki nan take, sai dai ko da aka sayo madara, bakin ya riga ya cije, saboda haka sai aka dauke ta zuwa bakin hanya aka sa ta a mota, amma da muka isa asibiti sai aka sanar da mu cewa ai ba ta da rai. Hakan ya tayar mana da hankali matuka, sai dai ba yadda muka iya, abin da Allah Ya kaddara ke nan,” inji shi.
Aminiya ta zanta da mahaifyar marigayiyar mai suna Hajiya Rakiya, sai dai a bayanin da ta yi, ta musanta zargin da ake yi na cewa guba ce A’isha ta sha. “Na ji mutane na ta magana a kan wannan lamari, amma ba gaskiya ba ce, dama ba ta da cikakkiyar lafiya,” inji ta.
Da aka tuntubi Babban Jami’in ’Yan sandan A Dibision da ke Suleja, CSP Sani Zubairu, ya ce ya ji labarin aukuwar lamarin, sai dai ya ce ba ya da masaniya a kan bayanin ko an maida karar zuwa ofishinsu.