Bazawarar da ta yi aure sau 10 tana ci gaba da neman mijin da ya dace

Wata bazawara mai shekara 56 wadda a yanzu ta rabu da mijinta bayan aurenta na 10, ta ce har yanzu ba ta daina shirin neman aure ba har sai ta samu mijin da ya dace da ita kuma masoyin mutu-ka-raba. Ta bayyana wa bazawarinta mai suna Dokta Phil, cewa ta rabu da mazan da ta […]

Bazawarar da ta yi aure sau 10 tana ci gaba da neman mijin da ya dace

Wata bazawara mai shekara 56 wadda a yanzu ta rabu da mijinta bayan aurenta na 10, ta ce har yanzu ba ta daina shirin neman aure ba har sai ta samu mijin da ya dace da ita kuma masoyin mutu-ka-raba.

Ta bayyana wa bazawarinta mai suna Dokta Phil, cewa ta rabu da mazan da ta aura ne saboda ba ta samu wanda ya dace da ita ba.

Hadimin Ganduje ya gwangwaje matasa da tallafin Jakuna

Mu Sha Dariya: Dunduma Dauda

“Idan har na yi aure na ga abu bai yi min ba, kuma ba zan lamunta ba, zan kasance ta farko in bayyana wa mijina cewa ya sake ni don mu rabu,” inji ta.

Bazawarar mai suna Cassey ’yar kasuwa ce ’yar kasar Amurka kuma ta samu nasarori a harkokin kasuwancinta.

A yanzu da take kokarin samun wani da za ta aura ta ce, ba ta damu ko sau nawa ta yi aure tana rabuwa da mazan ba, ba za ta daina neman aure ba har sai ta samu wanda zai rike ta da soyayya har abada.

Ta bayyana wa Dokta Phil cewa, aurenta na farko ta zauna a gidan aure na tsawon shekara takwas sannan suka rabu cikin mutunci, yayin da aurenta na biyu shi kuma ta yi zaman aure ne na shekara bakwai da kuma yin baiko na shekara biyu da rabi, inda ma’auratan suka samu da.

Ta ce amma sun fara samun matsala ce lokacin da mijinta ya daina furta cewa yana son ta.

Duk lokacin da Cassey ta furta wa mijin kalmar tana son sa, sai ya mayar mata ba yadda ta furta masa ba.

Sai dai Cassey ba ta yi cikakken bayani kan yadda ta rabu da mazan da ta aura daga na uku zuwa na goma ba.

Ta auri maza iri-iri wadanda suka hada da mai sha’awar shagaltuwa da mai son yin wa’azi, kuma tun tana kwaleji take neman wanda ya dace da ita da za su yi zaman aure amma ba ta samu ba, kamar yadda ta bayyana wa Dokta Phil.

Sai dai a cewar sabon bazawarin Cassey, zai kasance maigidanta wanda zai bar mata tarihi, yana kiran ta da sunan mai ba da umarni game da abin da take so.

Cassey ta kara da cewa, duk da rashin cika alkawarin da ake yi mata game da soyayyar da ake yi mata, ba za ta daina neman wanda zai rike ta da gaskiya da amana ba, za ta ci gaba da neman masoyin mutu-ka-raba.

Sojin sama sun yi kuskuren kashe mutum 16 a Zamfara

Rikicin Masarautar Kano: Tsagin Aminu Ado Bayero zai ɗaukaka ƙara

Yadda Jimmy Carter ya ceto rayuwata – Obasanjo

Sojoji sun lalata sansanin Bello Turji, sun kuɓutar da mutum 7