Bazoum ya maka masu juyin mulki a Kotun ECOWAS

Bazoum ya maka sojojin da suka yi masa juyin mulki a Kotun ECOWAS kan tsare shi da iyalinsa da suka yi ba bisa ka’ida ba

Bazoum ya maka masu juyin mulki a Kotun ECOWAS

Hambararren shugaban kasar Jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum ya maka sojojin da suka yi masa juyin mulki a kotun ECOWAS kan tsare shi da iyalinsa da suka yi ba bisa ka’ida ba.

Bazoum ya bukaci Kotun ECOWAS ta kwato masa ’yancinsa na walwala da dai sauran hakkokinsa na bil Adama, tare da matarsa, Hadiza Mabrouk Bazoum da kuma dansa Salem.

Tun a ranar 26 ga watan Yuli da sojojin da ke tsaron shugaban kasar Nijar suka yi juyin mulki, suke tsare Mista Bazoum da iyalinsa a fadarsa.

A karar da ya shigar ta hannun lauyansa, Maitre Mohamed Seydou Diagne, Bazoum ya bukaci kotun ta yi la’akari da yadda aka tauye musu ’yancinsu, ta umurci sojojin su gaggauta sakin su daga inda ake tsare da su.

Hambararren shugaban ya kuma bukaci Kotun ECOWAS din ta kuma yi la’akari da yadda masu juyin mulkin suka tauye wa mutunen da yake karewa ’yancin gudanar da harakokin siyasa.

A bisa haka ne ya roki Kotun ECOWAS ta tilasta wa ‘mai ikirarin zama shuagban kasa ko gwamnatin Nijar’ yin biyayya ga kundin tsarin mulkin kasar.

Wani na makusancin Bazoum, Dokta Haboubacar Manzo ya yaba da wannan mataki da ya kira na halin dattako.

Kawo yanzu dai Kotun ECOWAS ba ta tsayar da ranar sauararen shari’ar ba, ko da yake ta aike wa ma’aikatar shari’ar Nijer takarda don sanar da ita karar da ke gabanta.

Kawo yanzu gwamnatin sojin Nijar ba ta ce uffan game da wannan batu ba.

An ceto jaririyar da ’yar aikin gida ta sace a Edo

An ceto mutum 58 da aka sace a Kaduna

Sarkin Zazzau ya naɗa sabbin hakimai 7

Hajjin 2025: Maniyyata za su fara ajiye N8.4m a Kaduna