BBC ta yi kyakkyawan tanadi game da zaben Najeriya – Mansur Liman

Mansur Liman shi ne shugaban sashin Hausa na gidan rediyon BBC, a tattaunawarsu da Aminiya ya bayyana irin shirye-shiryen da suka yi wa masu sauraronsu dangane da yadda za su bayar da rahoto kan zaben 2015 da za a gudanar a watan nan: Aminiya: A yanzu ga shi zabe ya karato ko akwai wasu shirye-shiryen […]

BBC ta yi kyakkyawan tanadi game da zaben Najeriya – Mansur Liman
BBC ta yi kyakkyawan tanadi game da zaben Najeriya – Mansur Liman

Mansur Liman shi ne shugaban sashin Hausa na gidan rediyon BBC, a tattaunawarsu da Aminiya ya bayyana irin shirye-shiryen da suka yi wa masu sauraronsu dangane da yadda za su bayar da rahoto kan zaben 2015 da za a gudanar a watan nan:

Aminiya: A yanzu ga shi zabe ya karato ko akwai wasu shirye-shiryen da kuka kirkiro don masu sauraronku?
Mansur Liman: Tabbas akwai shirye-shiryen da muka kirkiro sakamakon karatowar zabe, za mu duba batutuwa masu yawa da suka hada da matsalar tsaro da abubuwan da suka dabaibaye hukumar zabe, za mu duba yadda za a gyara wadannan batutuwa. Za mu duba al’amuran da suka shafi jam’iyyu. Wadannan al’amura suna da yawa. Za mu tambayi jam’iyyun siyasa yadda za su mayar da hankali ga harkar tsaro da kiwon lafiya, yadda za a samar da ilimi da guraban aiki da sauransu. Mun fara shirin ne tun daga ranar 2 ga wannan wata. Ma’aikatanmu da ke aiko mana da rahotanni daga sassa daban-daban za su rika turo mana rahoto a kan wadannan batutuwa. Bayan haka wakilanmu za su shiga lunguna da sako da suka hada da karkara don jin ta bakin mutane, wakilanmu za su tambaye su wane abu za a yi musu su don a inganta rayuwarsu. Muna fata za mu samu amsoshi daga bakin mutane idan mun tambaye su.
Aminiya: Shin shirye-shiryen sun hada da rediyo da kuma talabijin ke nan?
Mansur Liman: Za a fi mayar da hankali ne a kan rediyo, na talabijin za mu fara a gobe 7 ga watan nan, tunda ka san muna da talabijin na Hausa da muke gabatar da shiri na minti 10 a kowace rana daga Litinin zuwa Juma’a, daga wannan ranar zuwa 15 ga wannan watan muna fatan za mu kawo wa masu sauraro da masu kallo kayatattun shirye-shirye. Akwai tattaunawa da ’yan siyasa game da irin alkawuran da suke yi, za su bayyana irin abubuwan da suke so su yi wa mutane, sannan bayan haka muna sa ran za mu samu hirarraki daga manyan ’yan siyasa, misali muna fatan za mu yi hira da dan takarar Shugaban kasa na Jam’iyyar APC, Janar Muhammadu Buhari, sannan muna fata za mu yi hira da shi kansa Shugaban kasa Goodluck Jonathan da ke takara a jam’iyya mai ci wato PDP, idan ba mu samu da Shugaban kasa ba sai mu yi da Mataimakinsa Namadi Sambo a madadinsa, musamman da yake Shugaban kasa ba ya iya magana da Hausa, idan kuma mun samu Shugaban kasa sai mu yi hira da shi, sannan mu fassara kalamansa don masu saurare su ji daga bakinsa.
Aminiya: Baya ga wakilan da kuke da su a fadin kasar nan ko za ku turo wakilai na musamman don su kawo rahoto a kan zabe?
Mansur Liman: Akwai ma’aikatanmu da za su zo Abuja don su taimaka mana, domin wannan aikin ba karamin aiki ba ne. A ranar da za a yi zaben Shugaban kasa shirinmu na rana da muke yi da karfe 3:00 agogon Najeriya da kuma na dare da muke yi da karfe 8:30, muna fatan za mu mayar da su awa daya kuma kai tsaye, inda za mu gabatar da su daga Najeriya, haka ma ranar da za a yi zaben gwamnoni wato ranar 28 ga watan Fabrairu, shi ma shirin rana da na dare za mu mayar da su awa 1. A wadannan shirye-shiryen za mu rika gabatar wa masu saurare abubuwan da suke faruwa a wurare da dama. Bayan nan a shafinmu na intanet muna fatan cewa za mu gabatar da wani shafi na musamman da zai kunshi abubuwan da suke wakana a lokacin da ake gudanar da zaben, wanda a Turanci ake kira ‘Libe Page,’ za mu fara shirin tun da safe har zuwa dare, idan kana da wayar salula za ka iya ganin abin da yake faruwa. Za ka ga a lokaci kaza abu kaza ne ya faru a wuri kaza. Iyakar wuraren da muke da wakilai iyakar abubuwan da za mu iya ke nan. Bayan haka akwai wani layin waya da muke so mu bayar wanda da shi za a yi whatsapp, da zarar mun bude wannan layin jama’a za su iya aiko mana hotuna ko bidiyon abubuwan da suke faruwa a wurarensu, za mu ga abin da ke faruwa, sannan mu tantance, idan mun tabbatar da hakikanin abin da yake faruwa sai mu watsa shi ga jama’a, za mu iya sanyawa ko a shafinmu na abin da ke faruwa kai-tsaye ko mu bayyana shi a shirye-shiryenmu na rediyo.
Sannan akwai shirinmu na ra’ayi-riga, za mu rika gabatar da shirye-shiryenmu kan batun barkewar tashin hankali kafin ko bayan zaben, za mu gabatar da shirin ne don mu tambayi jama’a mece ce fargabarsu game da zabe, mu tambaye su yadda za a magance barkewar tashin hankali. Za mu gayyato ma’aikatan tsaro don su bayyana mana irin matakan da za su dauka don magance tashin hankali a lokacin zabe, za mu gayyato ’yan siyasa don mu ji daga bakinsu don tabbatar da an gudanar da zabe lafiya cikin kwanciyar hankali.
Aminiya: A yawancin lokuta kafafen yada labarai sukan bayyana sakamakon zabe, inda hakan ya sanya ake samun matsala, wane shiri kuka yi don ganin an bayyana sahihin sakamakon zabe?
Mansur Liman: Ai sashin Hausa na BBC ba ma watsa sakamakon zabe a kan jita-jita, ko wanda ya fito daga wurin wani dan siyasa, akwai hukuma da doka ta bai wa ’yancin bayyana sakamakon zabe, wato Hukumar Zabe ta kasa ke nan, saboda haka ba za mu bayyana wani sakamakon zabe ba idan ba daga hukumar zabe ba ne, dole sai an tantance shi, an bayyana sakamakon zaben, tunda kun san ba kowace jiha muke da wakilan da za su kawo mana sakamakon zabe ba. Shi ya sa dole za mu samu sakamakon zabe ne a hedikwatar hukumar zabe, tunda a nan ne ake bayyana sakamakon zabe.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya