Belgium ta nada Tedesco a matsayin sabon kocinta
Tedesco zai sanya hannu har zuwa bayan kammala Gasar Nahiyar Turai ta 2024.
Kasar Belgium ta nada tsohon mai horar da kungiyar kwallon kafa ta RB Leipzig, Domenico Tedesco a matsayin sabon kocin da zai maye gurbin Roberto Martinez.
Hukumar Kwallon Kafa ta kasar Belgium, ta ce sabon kocin mai shekara 37, zai sanya hannu a kan kwantaragin har zuwa bayan lokacin Gasar Nahiyar Turai ta 2024, inda zai ja ragamar tawagar ’yan wasan kasar a wasan da za ta yi da Sweden a ranar 24 ga watan Maris, 2023.
- NAJERIYA A YAU: Yadda ’Yan Takara Ke Kashe Kudi A Lokacin Zabe
- Na san yadda zan farfado da tattalin arzikin Najeriya —Tinubu
An haifi Tedesco a Kasar Italiya, amma ya girma a kasar Jamus, sannan ya horar da kungiyoyin kwallon kafar Schalke 04 da Spartak Moscow.
“A ganina wannan babbar dama ce da zan horar da tawagar ’yan wasan Belgium.
“Na shirya tsaf don fara horar da su kuma ina farin ciki tun daga lokacin da muka tattauna,” in ji Tedesco.
Roberto Martinez dai ya ajiye aikinsa ne biyo bayan gaza fitowa daga matakin rukuni a Gasar Cin Kofin Duniya da aka yi a kasar Qatar a 2022.