Belin ’yan bunburutu

A makon da ya arce Madam In-yi-gwanjon-wala-wala da Gudun-wuni suka kulla yarjeejeniyar samar da albarkatun tunkuza, inda suka yi belin ’yan bunburutu masu buruntu satar mai. Wadannan jiga-jigan jami’an juya akalar matsabban kasar Haurobiya sun jinka wa ’yan bunburutu sama da Hauro gashin balama dari sili, wai don su cike gibin asarar da suka yi […]

Belin ’yan bunburutu

A makon da ya arce Madam In-yi-gwanjon-wala-wala da Gudun-wuni suka kulla yarjeejeniyar samar da albarkatun tunkuza, inda suka yi belin ’yan bunburutu masu buruntu satar mai. Wadannan jiga-jigan jami’an juya akalar matsabban kasar Haurobiya sun jinka wa ’yan bunburutu sama da Hauro gashin balama dari sili, wai don su cike gibin asarar da suka yi sanadiyyar zaftare darajar Hauro daGwamnan Babban asusun Haurobiya, Mista Gudun-wuni ya yi wuni-wunin tsuwurwurtawa.

Tun sa’adda aka sallamin Masanin Sisi-da-Sisi daga mukamin Gwamnan Babban Asusun Haurobiyawa, masu kwashi-kwaraf da dukiyar al’umma suka kara kaimin wajen raruke lalita, musamman ma ganin cewa idan har sun kyale tsohon gwamnan ya ci gaba da jan ragama, to za a yi ta yi musu tonon silili. Shi kuwa Gudun-wuni yana darewa bisa karaga sai ya shiga shirya wuni-wunin yadda za a wawushe dukiyar kasa. Don haka ya fara kassara Barau dan canji, inda ya bukaci ya zuba masa Hauro malala gashin tunkiya kofar hanci da babban lauje a asusun mara fa’ida, ko kuma a hana shi sana’a.
Bayan da Gudun-wuni ya yi rugu-rugu da Barau dan canji, sai kuma ya kassara darajar Hauro, ta yadda samarin kusu da ’yan matan jaba za su ji dadin jidar dukiyar Haurobiya. Kuma tunda wannan mai wuni-wunin ya dare bisa karagar juya akalar Hauron Haurobiya, jam’iyya mai dan boto da sanda jirge ta samu damar kara jefa al’umma cikin haure-haure da hauragiya.
’Yan makaranta, matukar ba ku kakaba wa kurungun ku tagiyar Malam Mantau, mun sha bijiro da darussan kan tsarin tsimi da ta’adi irin na bwamnatin Haurobiya, musamman ma yadda take aiwatar da tsarin lukudi da lakume kudi. Don haka masu fashi da mukami ko da dabara suka zarta ’yan fashi da makami wajen kassara al’umma. Masu koyon watsattsake da buda wagagen littattafai ya kmata ku fasko cewa, Hauron game garin Haurobiyawa darajarsa ta zabge, walau a lalilita ko a asusun ajiyar kasuwanci da suka hada Mai dakon mangalar Hauro a bayan giwa da mai ingarma Asusun assasa asarar Hauro mai lakabin korar kaza da mabudin dutse da santalelen asusun da asusu a babban titi. Shin abin tambaya a nan, wai zai yi wa talakawa cikon kashi sili da madambaci da aka zabge daga darajar Hauro, al’amarin da ya bai wa Dalar Hauron Amurkawa karin kima zuwa Hauro karamin lauje da karamin lauje da zagaye?
Haurobiyawa kun ga an yi belin ’yan bunburutu don kada su yi asara, ku kuma an kassara ku. Wannan kuwa duk ba wani abu ba ne illa tsarin Jarin hajijiya da talaka ko gumurzun gwabje al’umma. Kai hatta ’yan kwadago a ofisoshin gwmanati da na kamfanoni masu cin gasshin kansu, duk an kassara kimar darajar ladar kwadagon su; abin da kawai ya rage sai kowa ya bazama wajen laluben karin kadago.
An yi belin ’yan bunburutu, an jefa al’umma cikin balbalin bala’i. Duk da wannan beli da aka yi wa ’yan bunburutu, har yanzu akwai dogon tarragon kurkurido da shorido da baburido da ke neman cikan tumbinsu. Kuma kasancewar Haurobiya jamhuriyar ja-ni-ina-reto, wannan jimurda ta ’yan bunburutu masu buruntun satar mai ta kara jefa Haurobiya cikin duhun dundundum-durundum, inda su kuma ke ta cin duhu.
Haurobiyawa masu hankali a cikin kwanyarsu, ya kama ku fasko cewa, jam’iyya mai dan botoi da sanda jirge ta damalmala harkokin kasar nan, tunda tsarin damo-da-kura-da-diyya ya kange kowa daga kwasar garabasar dama-dama-da-kurda-kurdar was an Samson siya-siya. Shi ya sa kullum sai rokon ku suke da cewa ku kara jimiri da jinkirin cin jinbiri!
Lallai ya kamata mu yi karatun watsattsaken wasikar auran dawa da na gida, ta yadda za mu fasko kiren zuki-ta-malle kama kare ka hada shi da zomo da mahukuntan Haurobiya ke yi wa al’umma. Ba tare da na cika ku da surutru rututu ba, kamar Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters, mai rututun labarai, ya kamata mu tabbatar da cewa tonon sililin Farfesa Sallau Lado da watsattsaken wasikar Baba Ojo da watsattsaken Maimartaba Masanin Sisi-da-sisi duk batutuwa na na ingarman karfen karafa.
Mu bai wa Farfesa Ja-gaban zabi-sonka hadin kai, wajen amfani da Katin raddi ga masu magudi da murgude kuri’u. Mu nemi tsari daga Mugun daji Dauda-mai-maki, don kada ya make mu. Su Fufffuken Fankan-fayau, mu hanzarta mu jefa su a turu, tun kafin su bi Baudadden Joji, su called a zarar an tuntsirar da jam’iyya mai dan boto da sanda jirge, a rana ta karamin lauje da madambaci ga watan Marisa na shekara ta dubu karamin lauje da sili da babban lauje.
Haurobiyawa sai a daura damara wajen wancakalar da ’yan gwanjo, wadanda ke belin ’yan bunburutu, su tamke talakawa da sasarin talauci; kada mu bayar da dama ga wadanda suka mayar da kasa ta zama ba tsaro, sai tsoro, inda kullum sai wutar rikicin haramta bobo da kwambon bokoko ke ruruwa. Wadannan duk kadan ne daga miyagun ayyukan da jiga-jigan mai dan boto da sand ajirge ke tsuwurwurtawa. Kodayake mun yi sa’a, tunda Banga-banga Tukururu ya take ta-mola, sai kuma ga Dumu-dumu Muzu-muzu ya sauya wasa. Miyagu sun fara cin kasa, a daidai lokacin da talakawan Haurobiya za su fara kwasar wasa-wasa gami da masa a kwanon tasa.