Bello BMB ya bukaci Isra’ila ta daina kai hare-hare a Gaza
Fitaccen Darakta kuma jarumin fina-finan Hausa Bello Muhammad Bello (BMB)ya bukaci Isra’ila ta daina kai hare-hare a Gaza.Jarumin ya sanya hotonsa a shafin twitter, inda yake rike da wata takarda mai ruwan shudi da aka yi rubutu da Turanci kamar haka: “Killing The Innocents is TERRORISM. Stop The Massacre IN GAZA.” Inda hakan yake nufin: […]
Fitaccen Darakta kuma jarumin fina-finan Hausa Bello Muhammad Bello (BMB)ya bukaci Isra’ila ta daina kai hare-hare a Gaza.
Jarumin ya sanya hotonsa a shafin twitter, inda yake rike da wata takarda mai ruwan shudi da aka yi rubutu da Turanci kamar haka: “Killing The Innocents is TERRORISM. Stop The Massacre IN GAZA.” Inda hakan yake nufin: “Kashe wadanda ba su ji ba su gani ba ta’addanci ne. A daina kisan kiyashi da na kare dangi a Gaza.
Ya bayyana cewa ci gaba da hare-haren zai ci gaba da yada kyama a tsakanin Musulmi da wadanda ba musulmi ba.