Bello El-Rufai ya fice daga APC zuwa ADC

A cikin wata sanarwa da Bello El-Rufai ya wallafa a shafinsa na sada zumunta ya ce ya yi hakan ne don koyi da mahaifinsa Nasir El-Rufai.

Bello El-Rufai ya fice daga APC zuwa ADC

A zaman Majalisar Wakilai na tarayya da aka yi ranar Alhamis Shugaban Majalisar, Tajudeen Abbas GCON, ya sanar da zauren sauya shekar Ɗan majalisar Tarayyar mai wakiltar Kaduna ta Arewa, Bello El-Rufai daga jamʼiyyar APC zuwa ADC.

A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta ya ce ya yi hakan ne don koyi da mahaifinsa Nasir El-Rufai.

Bello El-Rufai ya ƙara da cewa, “A yanzu ni mamba ne a jam’iyyar ADC, kuma zan nemi sake tsayawa takara domin ci gaba da wakiltar mutanen mazaɓar Kaduna ta Arewa a ƙarƙashin wannan jam’iyya.”

Ina tare a wannan sabon shafi da babban dattijonmu, Hon. Engr. Suleiman Richifa, mai wakiltar Soba, da kuma dan uwana, Hon. Umar Ajilo, mai wakiltar Makarfi/Kudan, waɗanda duka suka sauya sheƙa daga tsofaffin jam’iyyunsu zuwa jam’iyyar ADC.