Bello Halliru ya gurfana a gaban kotu a keken guragu
Tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP ta kasa Alhaji Mohammed Bello Halliru ya halarci zaman Babban Kotun Tarayya da ke Abuja, domin amsa tuhuma kan zargin da ake yi masa na hannun a badakalar karkatar da kudin sayo makamai da ake zargin Ofishin tsohon Mashawarcin Shugaban kasa Sambo Dasuki da jagoranta.Wata majiya ta ce an kama Bello […]
Tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP ta kasa Alhaji Mohammed Bello Halliru ya halarci zaman Babban Kotun Tarayya da ke Abuja, domin amsa tuhuma kan zargin da ake yi masa na hannun a badakalar karkatar da kudin sayo makamai da ake zargin Ofishin tsohon Mashawarcin Shugaban kasa Sambo Dasuki da jagoranta.
Wata majiya ta ce an kama Bello Halliru ne a watan Disamban da ya gabata kan zargin ya karbi Naira miliyan 600 daga ofishin Dasuki ta amfani da wani kamfanin harkokin gine-gine mai suna Bam Properties. Kudin a cewar Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin kasa (EFCC), yana daga cikin Dala biliiyan biyu da miliyan 100 na kudin makamai da aka ware domin saya wa sojoji makamai a zamanin gwamnatin da ta gabata. An so gabatar da Bello Halliru ne a gaban kotun a makon jiya, amma hakan ba ta samu ba saboda rashin lafiyarsa.
Dokta Bello Halliru ya gurfana a gaban kotunne tare da dansa Abba Bello, bayan da Hukumar EFCC ta gabatar da tuhume-tuhume guda hudu da suka shafi almundahanar kudi a kan dan siyasar da dansa a ranar 26 ga Disamban da ya gabata.
Ana zargin Abba Mohammed Bello ne ya karbi Naira miliyan 600 daga ofishin Mashawarcin Shugaban kasa kan Harkokin Tsaro a madadin Kamfanin Bam Properties.
Sai dai Dokta Bello Halliru da dansa Abba, sun musanta zarge-zargen da ake yi musu. Kuma lauyan Abba Mista Ogala Osoka ya rubuta takardar neman a bayar da belin wanda yake karewa zuwa lokacin da za a ci gaba da sauraren karar.
Shi ma lauyan tsohon Shugaban na PDP, Abdul’azeez Ibrahim ya roki kotun ta yi amfani da bukatar beli ta farko kan wanda yake karewa. Ya shaida wa kotun cewa, Bello Haliiru yana Landan inda aka yi masa tiyata, amma da ya gano zarge-zargen da ake yi masa da sharuddan da aka gindaya masa, sai ya yanke shawarar dawowa kasar nan, kuma an yi masa jinya a asibitin Abuja saboda tiyatar da aka yi masa sabuwa ce. Ya gabatar da shaidu a kan haka da suka hada da wasika daga likitan da ke yi masa jinya da kuma wasu hotuna yana jinya.
Sai dai mai gabatar da kara Aliyu Yusuf ya roki kotun ne da kada ta bayar da belin da lauyoyin biyu suka nema, inda ya ce laifuffukan da ake zargin mutanen biyu suna da tsanani, kuma wanda ake zargi na farko a takardarsa ta neman beli ba nuna cewa ba za a iya kula da lafiyarsa a gidan kurkuku ba.
Bayan sauraren muhawarar lauyoyin ne alkalin kotun Mai shari’a Ahmed Mohammed ya ce a sakaya Abba a kurkukun Kuje, yayin da ya mika kula da Bello Halliru a hannun Sufeto Janar na ‘’Yan sanda Najeriya a yayin da yake gadon asibiti.