Bello Maitama Yusuf ya rasu
Allah ya yi wa Sardaunan Dutse, Sanata Bello Maitama Yusuf rasuwa da safiyar Juma’a a Kano. Marigayin ƙwararran lauya ne wanda ya yi minista a jamhuriya ta biyu kuma ya zama sanata a jamhuriya ta huɗu. Ya rasu ya na da shekaru 76 bayan gajeriyar rashin lafiya. Mutum 20 da Shata ya fito da su […]

Allah ya yi wa Sardaunan Dutse, Sanata Bello Maitama Yusuf rasuwa da safiyar Juma’a a Kano.
Marigayin ƙwararran lauya ne wanda ya yi minista a jamhuriya ta biyu kuma ya zama sanata a jamhuriya ta huɗu.
Ya rasu ya na da shekaru 76 bayan gajeriyar rashin lafiya.
Mutum 20 da Shata ya fito da su a waka
Ya bar mata biyu da ƴaƴa 10, maza biyar, mata biyar.
Za a yi jana’izarsa bayan Sallar Juma’a a Fadar Sarkin Kano.