Bello Turji Ya Nemi Sulhu Da Gwamnati 

Shahararren ɗan ta’adda Bello Turji na afuwa da sulhu da gwamnati, kwanaki kadan bayan sojoji sun kashe uban gidansa Halilu Sabubu.

Bello Turji Ya Nemi Sulhu Da Gwamnati 

Bello Turji

Shahararren ɗan ta’adda a Jihar Zamfara Bello Turji na neman sulhu da gwamnati, kwanaki kadan bayan sojoji sun kashe uban gidansa Halilu Sabubu.

Bello ya kuma nemi gwamnatin Zamfara ta sanya shi cikin kokarinta na samar da zaman lafiya a jihar.

Turji ya sanar da haka ne a wani bidiyo da ya yi bayan sojoji sun kashe Halilu Sububu.

A baya-bayan nan jami’an tsaro sun hallaka manyan jagororin ’yan bindiga a Zamfara.

Haka ta faru ne musamman bayan tsohon gwamna jihar kuma Karamin Ministan Tsaro, Muhammad Bello Matawalle da manyan kwamandojin soji sun tare a can da nufin ganin bayan ayyukan ’yan fashin daji.

A jihohin Kaduna da Katsina da Neja ma wasu gawurtattun ’yan bindiga sun gamu da ƙarar kwana a lokuta daban-daban a baya-bayan nan.

A cikin bidiyon Turji na ta’aziyyar Halilu Sububu, an ji shi yana cewa ragargazar da sojoji suka yi ba za ta sa su saduda ba.

Amma sai ya ƙara da neman afuwa da sulhu inda ya nemi gwamnatin ta zo su zauna su tattauna a fahimci juna, wanda a cewarsa, hakan zai samar da zaman lafiya a Zamfara da ma ƙasa baki ɗaya.

A ’yan baya-bayan nan sojojin Najeriya na ci gaba da samun nasara a yaƙinsu da ’yan bindigar da yaƙi ci yaƙi cinyewa shekara da shekaru.

Kazalika rikici tsakanin ƙungiyoyin ’yan fashin daji ya yi sanadiyyar mutuwar wasu manya daga cikinsu tare da yaransu.

Abba ya yi tafiya yayin da rikici ya dabaibaye NNPP a Kano

Kotu ta hana EFCC kama tsohon minista kan taƙaddamar fili

Isra’ila ta ɗaiɗaita yara sama da 400,000 a Lebanon — UNICEF

Ba zan ce uffan kan rikicin NNPP a Kano ba — Kwankwaso