Bene mai hawa 4 ya rufta da mutane a Abuja
An ceto su daga baraguzan bene mai benen da ya rushe da su aAbuja
An ceto mutane uku bayan wani bene mai hawa hudu ya rushe a Abuja.
Wasu mutane da dama sun makale a cikin bene da ya rushe a yankin Area 11 da ke unguwar Garki.
Ranar Litinin da misalin karfe 8;30 na dare ne ginin ya rushe, jim kadan bayan wasu leburori da ke aiki a wajen sun tashi.
Wani mazaunin unguwar Garki, Joseph Habila, ya ce karar rushewar ginin ta haifar da zullumi a tsakanin mazauna yankin.
- An tube wa ’yan sanda 5 kaki kan kwatar kudi a shingen bincike
- NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Magance Kuncin Da ‘Yan Najeriya Suke Ciki
Joseph ya ce, “Allah ne Ya kiyaye saboda Ni kaina na je na yi sayayya a kusa da ginin, ban jima sa barin wurin ba ginin ya rushe.”
Ya ce jami’an tsaron da suka kai dauki sun ceto mutanen da suka makale a cikin baraguzan ginin.
Sai dai ya ce na zai iya tantance adadin wadanda aka ceto ba.
Rundunar ’yan sandan Abuja ta sanar cewa an ceto mutane uku daga baraguzan.
Sanarwar da kakakin rundunar, Josephine Adeh ta fitar ta ce an garzaya da mutanen zuwa asibiti domin ba su kulawar da ta dace.
Ta kara da cewa an sanar da hukumomin da suka dace game da al’amarin kuma sun karbe ikon wurin da abin ya faru.