Benitez ya zama sabon kocin Madrid

A shekaranjiya Laraba ne kulob din Real Madrid da ke Sifen ya bayyana Rafael Benitez, tsohon kocin Napoli da ke Italiya a matsayin sabon koci. Kulob din ya gabatar da sabon kocin ne a gaban dubban magoya bayansa a filin wasansa mai suna Santiago Bernabeu.dan kimanin shekara 55, Benitez dai ya maye gurbin tsohon koci […]

Benitez ya zama sabon kocin Madrid
Benitez ya zama sabon kocin Madrid

A shekaranjiya Laraba ne kulob din Real Madrid da ke Sifen ya bayyana Rafael Benitez, tsohon kocin Napoli da ke Italiya a matsayin sabon koci.

Kulob din ya gabatar da sabon kocin ne a gaban dubban magoya bayansa a filin wasansa mai suna Santiago Bernabeu.
dan kimanin shekara 55, Benitez dai ya maye gurbin tsohon koci Carlo Ancelotti ne da kulob din ya raba-gari da shi kimanin makwanni biyu da suka wuce bayan an gama gasar La-Ligar Sifen ta bana.
Idan za a tuna, Benitez dai ya fara harkar horarwa ne a kulob din Madrid, inda ya horar da kulob din matasa kafin ya zama kocin kulob din balencia da ke Sifen inda ya samu nasarar lashe wa kulob din kofin La-Liga har sau biyu.
Baya ga haka Benitez ya horar a kulob da dama da suka hada da Liberpool da na Chelsea a Ingila da kuma Inter Milan da Napoli a Italiya.
Kocin ya shafe shekara biyu yana horarwa a kulon din Napoli na Italiya amma sun raba gari da kulob din a karshen makon jiya bayan kulob din ya sha kashi a wajen na Lazio da ci 4-2 a gasar rukunin Serie A na Italiya.
Tsohon kocin Madrid Ancelotti dai ya shafe kimanin shekara biyu a kulob din, kuma ya samu nasarar lashe kofuna hudu a kulob din kafin a sallame shi a karshen kakar wasa ta bana.
Masana harkar kwallo sun yi hasashen sai Benitez ya yi da gaske wajen lashe wa Madrid manyan kofuna muddin yana son ya zauna a kulob din, don kulob ne da ba kasafai yake jure rashin nasara ba tare da ya kori kocin da ke horar da ’yan kwallonsa a kowane lokaci ba.