Benzema, Mbappe da Messi na takarar gwarzon FIFA na 2022

FIFA za ta gudanar da bikin karrama gwarzonta a ranar 27 ga watan Fabrairun 2023.

Benzema, Mbappe da Messi na takarar gwarzon FIFA na 2022

Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya FIFA, ta bayyana Karim Benzema da Lionel Messi da Kyalin Mbappe a matsayin masu takarar gwarzon dan kwallon kafa na duniya na 2022.

Ana iya tuna cewa, Benzema na da kwallo 15 da ya ci a Gasar Zakarun Turai na Champions League da ya kai Real Madrid ta lashe kofin na 13 jumulla.

Shuraim ya yi murabus daga limanci a Masallacin Harami

CBN ya wadata Najeriya da sabbin takardun kudi ko a ci gaba da juya tsofaffi —Majalisar Koli

Haka kuma tsohon dan kwallon tawagar Faransa shi ne kan gaba a yawan zura kwallaye a raga a La Liga a bara.

Shi kuwa Mbappe, wanda PSG ta lashe Ligue 1 a bara ya ci kwallo 26 a wasa 46 da ya yi wa kungiyar Faransa.

Ya kuma taka rawar gani a Gasar Kofin Duniya da aka yi a Qatar, inda ya lashe takalmin zinare  na gasar a matsayin dan wasan mafi zura kwallaye.

Mbappe ya yi bajintar gaske inda ya ci kwallo uku a wasan karshe na Gasar Kofin Duniya da Argentina ta yi nasara a bugun fenariti.

Messi kyaftin din Argentina babu laifi ya dan tabuka taka rawar gani a PSG tun bayan da ya koma Faransa da taka leda daga Barcelona a 2021.

Ya bayar da gudunmuwar da PSG ta lashe Ligue 1 a kakar farko da ya buga mata tamaula.

Shi ne ya ja ragamar Argentina ta lashe Kofin Duniya, kumq shi aka bai wa fitaccen dan wasa a babbar gasar tamaula ta duniya ta 2022.

Za a karrama fitaccen dan wasan tamaula na duniya a bana, kan rawar da ya taka tsakanin 8 ga watan Agustan 2021 zuwa 18 ga watan Disambar 2022.

Za a sanar da gwarzon dan kwallon kafa na duniya na FIFA a bikin da za a gudanar ranar 27 ga watan Fabrairun 2023.

An tace ukun daga 14 da aka bayyana a baya, inda aka sa wasu kwararru suka tankade su zuwa ukun karshe da za a fidda gwani.

Za kuma a gudanar da zaben tsakanin koci-koci na tawagar mambobin FIFA da kyaftin-kyaftin da wasu ’yan jarida da kuma kada kuri’a a yanar gizo ta FIFA.