Benzema na Madrid ya samu rauni

Rahotanni da ke fitowa daga kulob din Madrid sun ce Karem Benzema ya shiga sahun ’yan kwallon kulob din 8 da suka ji ciwo a kakar wasa ta bana. ’Yan kwallon da suke jinya a yanzu haka a kulob din sun hada da Marco Assensio da Jesus Ballejo da Gareth Bale da Toni Kroos da […]

Benzema na Madrid ya samu rauni

Rahotanni da ke fitowa daga kulob din Madrid sun ce Karem Benzema ya shiga sahun ’yan kwallon kulob din 8 da suka ji ciwo a kakar wasa ta bana.

’Yan kwallon da suke jinya a yanzu haka a kulob din sun hada da Marco Assensio da Jesus Ballejo da Gareth Bale da Toni Kroos da sauransu.

Benzema ya karye ne a yatsarsa ta dama a ranar Lahadin da ta wuce lokacin da kulob din Madrid yake fafatawa da na Real Betis a gasar La-Liga ta Sifen.

Tun a zangon farko na wasan ne Benzema ya samu rauni, wanda hakan ya sa ba a dawo da shi daga hutun rabin lokaci ba.

Madrid ce ta samu nasara a wasan da ci 2-1.

Rahoton da kulob din ya sanar ya nuna Benzema zai shafe akalla mako uku yana jinya.

Jesus Ballejo, dan kwallon baya a Madrid shi ma ya ji ciwo ne a ranar Litinin da ta gabata lokacin da suke atisaye, al’amarin da ya sa ya fashe da kuka ganin wannan shi ne karo na 4 da yake jin rauni a kakar wasa ta bana. Sau biyu kacal ya yi wa Madrid kwallo a kakar wasa ta bana saboda yawan jin rauni.

Saboda yawan ’yan kwallon da suka ji rauni a Madrid ya sa kulob din yake tangal-tangal a kakar wasa ta bana, musamman a gasar La-Liga, inda kawo yanzu kulob din FC Barcelona da ke jan ragamar gasar ya ba Madrid tazarar maki 10 tun ba a je ko’ina ba.