Benzema ya kwaci Real Madrid a hannun Sevilla
Real Madrid ta farko kwallaye biyu ta kara wa Sevilla a gasar La Liga
Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta kwaci kanta da kyar a hannun Sevilla a gasar La Liga a karawarsu ta daren ranar Lahadi.
Babban dan wasan Real Madrid, Karim Benzema, ne ya kwace ta bayan an kusa tashi wasan a kunnen doki, a wasan da Sevilla ta fara zura wa kungiyar kwallo biyu da nema.
Barayi sun fasa gidan Benzema lokacin da Madrid ke wasa
Real Madrid ta tallafa wa yaran da yakin Ukraine ya mayar ’yan gudun hijira
A farkon wasan, Sevilla ta rike wa Real Madrid wuta, har zuwa zagaye na biyu tana kan gaba.
Ana ganin rashin katabus din Real Madrid a farkon wasan na da nasaba da tasirin dukan da ta sha a Gasar Zakarun Turai a baya-bayan nan.
Sai dai kuma da aka dawo zagaye na biyun wasan, Real Madrid ta gyagije ta dagula wa Sevilla lissafi, inda ta farke kwallayen biyu. daga nan kuma suka ci gaba gumurzu, a yayin da lokacin tashi yake kara karatowa.
Bayan an yi ta fafatawa a haka ne, ana dab da tashi wasan gaban Real Madris, Karim Benzema, ya zura kwallo na uku a ragar Sevilla, a haka aka tashi wasan, tana da ci 3, Sevilla kuma 2.