Bera ya lalata takardun kudi da suka kai Naira miliyan shida da rabi a injin ATM
Wani mai gyaran injin cire kudi (ATM) da aka kira don duba matsalar da take sanya rashin aikin injin na tsawon kwanaki, bayan gudanar da bincikensa kan abin da ke hana injin fitar da kudi, ya ce sai ya fara jin warin bera a cikin injin. Beran wanda ke yankin Assam na kasar Indiya ya […]
Wani mai gyaran injin cire kudi (ATM) da aka kira don duba matsalar da take sanya rashin aikin injin na tsawon kwanaki, bayan gudanar da bincikensa kan abin da ke hana injin fitar da kudi, ya ce sai ya fara jin warin bera a cikin injin.
Beran wanda ke yankin Assam na kasar Indiya ya kutsa cikin injin ATM ne ya kuma lalata kudin da ke ciki da suka kai Dala dubu 18 a kudin kasar Indiya wato Rupee wanda ya yi daidai da Naira miliyan 6 da dubu 660 a kasuwar bayan fage, daga bisani ya mutu a cikin injin, kamar yadda jami’an bankin SBI na Indiya suka sanar.
Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ruwaito cewa, injin ATM din ya dauki kwanaki ba ya aiki wanda ya tilasta wa ma’aikata zuwa injin ATM din domin dubawa da shawo kan matsalar. Da zuwansu ne suka iske tarin takardun kudin daga bisani kuma sai ga mataccen bera a karkashin dalar takardun kudin.
Manajan bankin SBI na shiyyar, Chandan Sharma ya ce: “ATM din ya kwana biyu ba ya aiki amma yayin da ma’aikatammu suka bude kofar ma’adanar kudin sai suka tarar da mataccen bera da kuma tarin yagaggun takardun kudi kaca-kaca. Abin ya ba mu mamaki sosai, kuma muna bincike don kiyaye faruwar hakan a nan gaba”.
Beran dai kamar aka ruwaito, karami ne wanda hakan ya ba shi damar kauce wa kyamarar tsaro da ke cikin injin kuma ya lalata Dala 17,662 daidai da Naira miliyan (6,400,355.56) na jimillar kudin Dala dubu 42,685 daidai da Naira miliyan (15,468,190.30) da ke ciki. Mushen beran har ya bushe lokacin da aka fito da shi.
Duk da cewa kyamarar ba ta gano beran ba yayin da yake shiga cikin injin, mahukunta sun tabbatar da cewa wannan asarar da aka ba wani ya aikata ba illa beran da ya shiga cikin injin.