Beraye sun kacaccala kudi a ATM

A babban birnin Kazakhastan, Astana , wasu beraye biyu su kutsa cikin na’urar zaro kudi ta ATM, inda suka fake daga kankara, amma ma’aikatan bankin da suka gano su sun yi matukar kaduwa ganin yadda suka yi kaca-kaca da kudi,lokacin da aka zo zuba kudi a na’urar. Sun dauki bidiyon jabar da irin barnar da […]

Beraye sun kacaccala kudi a ATM

A babban birnin Kazakhastan, Astana , wasu beraye biyu su kutsa cikin na’urar zaro kudi ta ATM, inda suka fake daga kankara, amma ma’aikatan bankin da suka gano su sun yi matukar kaduwa ganin yadda suka yi kaca-kaca da kudi,lokacin da aka zo zuba kudi a na’urar.

Sun dauki bidiyon jabar da irin barnar da suka yi da kashinsu. A bidiyon da aka baza a shafukan intanet, ana jin wata murya na cewa “A nan muna da jaba. daukacin miyagu masu kurmusu ’yan mafia,” daidialokacin da ma’aikatan bankin suke daga rufin akwatin kudin da aka yi musu kaca-kaca. Bidiyon ya nuna beraye lokacin da ake janye daurin kudin zuwa gefe, sai daya daga cikin matan da ke aikin abankin ta dan yi kara cikin kaduwa.

Bankin dai bai bayyana yawan kudin da berayen suka lalata ba, amma kafar yada labaran kkasar ta kimanta kudin da kimanin daurin Dala 300.