Bianca Ojukwu ta yaba wa kulob din Rayo ballecano kan karramawar da ya yi wa golansu dan Najeriya da ya mutu

Ambasadar Najeriya a Sifen Misis Bianca Odumegwu Ojukwu ta yaba wa kulob din El-Rayo ballecano da ke Sifen saboda irin karramawar da kulob din ya yi wa gawar tsohon golansu, dan Najeriya mai suna Wilfred Agbonabbare wanda ya rasu a watan jiya a Sifen. Golan ya rasu ne bayan ya yi doguwar jinya bayan ya […]

Bianca Ojukwu ta yaba wa kulob din Rayo ballecano kan karramawar da ya yi wa golansu dan Najeriya da ya mutu
Bianca Ojukwu ta yaba wa kulob din Rayo ballecano kan karramawar da ya yi wa golansu dan Najeriya da ya mutu

Ambasadar Najeriya a Sifen Misis Bianca Odumegwu Ojukwu ta yaba wa kulob din El-Rayo ballecano da ke Sifen saboda irin karramawar da kulob din ya yi wa gawar tsohon golansu, dan Najeriya mai suna Wilfred Agbonabbare wanda ya rasu a watan jiya a Sifen. Golan ya rasu ne bayan ya yi doguwar jinya bayan ya kamu da cutar kansa.

Jakadar ta bayyana farin cikinta ne a lokmacin da ta halarci bikin bizne tsohon dan kwallon a makabartar Meco da ke yankin Alcala a Sifen a ranar 29 ga watan Janairun wannan shekara da muke ciki.
Ta ce ta yaba da yadda kulob din ya karrama tsohon dan kwallon inda ya amince a bize ne shi a Sifen ba tare da an mayar da gawarsa gida Najeriya ba.
“Wannan abu ya yi matukar faranta mini rai don da haka sauran kulob suke yi da ba a samu matsala ba idan an samu rasuwar ’yan wasa”, inji ta.
Jakadar ta halarci filin wasan kulob din ne tare da wasu daga cikin ’yan Najeriya mazauna Sifen don yi wa gawar dan kwallon ban-kwana kafin a binne ta.
Shi dai tsohon golan kulob din Rayo ballecano Willie Agbonabbare ya rasu ne bayan ya yi fama da ciwon kansa (cancer) na tsawon lokaci. Kuma yana zaune ne a Sifen tare da iyalinsa.