Bianou: Al’ada ko addini?

A birnin Agadas an yi takaddama kan kimar bikin Bianou a matsayin al’ada ko addini, inda Shugaban Bianou, Attah Tambari da masu ra’ayi irin nasa suka rinjaya da cewa al’ada ce, amma masana irin su Sardaunan Abzin, Dokta Abdulkadir Labaran sun jajirce a kan ra’ayin cewa Bianou addini ne.Attah Tambari, ya bayyana cewa Kalmar Bianou […]

Bianou: Al’ada ko addini?

Sardaunan Abzin tare da Mai alfarma Sarkin Musulmin Nijar, Sultan Omar Ibrahim OmarA birnin Agadas an yi takaddama kan kimar bikin Bianou a matsayin al’ada ko addini, inda Shugaban Bianou, Attah Tambari da masu ra’ayi irin nasa suka rinjaya da cewa al’ada ce, amma masana irin su Sardaunan Abzin, Dokta Abdulkadir Labaran sun jajirce a kan ra’ayin cewa Bianou addini ne.
Attah Tambari, ya bayyana cewa Kalmar Bianou a yaren Abzinanci tana nufin ‘safiyar rawa,’ don haka ma daukacin ’yan masarautar Abzin ke kwasar rawa tare da kidin mandirinsu na ‘Akazam.’ Kuma ya yi nuni da cewa matukar al’ummar Agadas, musamman matasa suka yi sakaci, Bianou ta kubuce musu, to tabbas babu abin da ya yi saura na al’adun al’ummar garin. ‘Sannan akwai yiwuwar a ce Agadas ta lalace, idan har babu Bianou.’
Ita ma uwargidan Attah Tambari, Ummu Amina, Bututuwa, ta ce duk wadanda suka saki Bianou, ‘ba ’yan Agadas ba ne.’ Kuma ta yi nuni da fifikon darajar tufafin al’ada da ratayen alabe da suke a matsayin sutura mafi kima, wadda ta fi atamfa, musamman a ranar bikin Bianou.
Shi kuwa, Sardaunan Abzin, Dokta Abdulkadir Labaran Koguna cewa ya yi, Bianou addini ne, domin ana gudanar da bikin a farkon watan kalandar hijira ta Musulunci. “Ana yin ta ne don tunawa da Hijirar Manzon Allah (SAW) daga Makka zuwa Madina. Kuma da mandarin Akazam da kwatankwacinsa aka tarbe shi, ana ta daga ganyen dabino. Kuma tarbiyya ce ta addini Musulunci. Bisa wannan dalili nike ganin Bianou na da tushe a addini,” inji shi.
Su kuwa gungun ’yan Najeriya, wadanda suka hada da Aminu Sadi Bello da Alhaji Auwalu Babba dandago da Malam Usman Musa Gabari, sun tabbatar da cewa, Bianou al’ada ce da ake danganta ta da addini, saboda haka aka yi mata kyakkyawan riko, amma ba addini ba ce.
“Da Bianou addini ne, ai da an rika gudanar da ita a daukacin fadin duniya,” a cewar Aminu Sadi Bello, tsohon Shugaban Majalisar Kansiloli a karamar Hukumar Gwale ta Jihar Kano, wanda kuma ya kasance daya daga cikin mutanen da suka halarci bikin Bianou a bana. “Ka ga a Agadas akwai mutanen da ba su barin ’ya’yansu su halarci wurin bikin Bianou. Don haka ina ganin akwai yiwuwar bikin ya rika ja da baya,” inji shi.
Wannan biki dai ya fi bayar da fifiko kan gasar raye-raye da kade-kade a tsakanin Abzinawan Gabas da na Yamma, addini kuwa ya fi bayar da fifiko ne wajen karance-karancen litattafan ilimi da aiwatar da ayyukan ibada, don biyayya ga Mahalicci. Don haka an hakkake cewa Bianou ba addini ba ne, illa dai kawai al’ada ce da aka shigo da ita cikin rigar addinin Musulunci, ta hanyar fakewa da hijirar Manzon Allah (SAW) da kidayar watannin Musulunci.