Bichi ba masaka tsinke yayin ba Sarki Nasiru Ado Bayero sandar mulki

Bikin na zuwa ne kwana daya bayan Sarkin ya aurar da ’yarsa ga dan Shugaba Buhari.

Bichi ba masaka tsinke yayin ba Sarki Nasiru Ado Bayero sandar mulki

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje yayin da yake ba Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero sandar mulki

Hoto: Sani Maikatanga

Dubun-dubatar mutane ne suka yi wa garin Bichi tsinke domin shaida mika wa Sarkin garin, Alhaji Nasiru Ado Bayero sandar mulki da Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranta.

Taron, wanda ya gudana ranar Asabar a filin wasa na garin na Bichi, na zuwa ne kwana daya bayan Sarkin ya aurar da ’yarsa, Zahra ga dan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Yusuf a ranar Juma’a.

Bichi dai na daya daga cikin sabbin masarautu hudun da Gwamna Ganduje ya kirkiro a Jihar a shekarar 2019.

Da yake jawabi a wajen taron, Shugaba Buhari, wanda Shugaban Ma’aikatan Fadarsa, Farfesa Ibrahim Gambari ya wakilta, wanda kuma baffa ne ga Sarkin, ya bayyana ziyarar tasa a matsayin ta gida.

Farfesa Gambari wanda ya bayyana kirkirar sabbin masarautu a Jihar a matsayin wani gagarumin yunkurin kawo ci gaba, ya kuma yi fatan alheri ga Sarkin tare da kiranshi kan ya samar da shugabanci abin koyi.

Shi kuwa Gwamna Ganduje cewa ya yi taron cike yake da tarihi kasancewar rabon da a irinsa sama da shekara 50 kenan, in ban da a shekarar 2014.

Ya ce, “Na san mai martaba Sarki gogaggen ma’aikaci ne, saboda haka ina kira gare shi da ya yi amfani da tarin ilimi da gogewarsa wajen ciyar da masarautarsa gaba da kuma hada kan jama’a.”

Da yake mayar da nasa jawabin, Sarki Nasiru Bayero ya yi alkawarin ba mara da kunya ta hanyar bin tafarkin magabata wajen sauke nauyin da aka dora masa.

Ya ce, “Za mu hada kai da gwamnatoci a dukkan matakai wajen kawo wa jama’a ci gaba, musamman ta bangaren samar da hanyoyi, ruwan sha da rijiyoyin burtsatse da gina masallatai da makarantun boko da na Islamiyya da kuma yaki da talauci.

“Ya kamata kuma mu mayar da hankali wajen kare muhalli da kauce wa kwararowar hamada ta hanyar daddasa bishiyoyi ,” inji Sarkin.

Farfesa Gambari dai shi ne ya jagoranci tawagar Gwamnatin tarayya a taron, wacce ta kunshi Ministocin Tsaro da na Noma da Raya Karkara da na Ruwa da na Harkokin Sufurin Jiragen Sama da kuma kakakin Shugaban Kasa, Malam Garba Shehu.

Kazalika, Gwamnonin Jihohin Neja; Abubakar Sani Bello; da na Kogi, Alhaji Yahaya Bello da tsohon Gwamnan Imo, Sanata Rochas Okorocha da Shugaban Hukumar Tsaro ta DSS, Yusuf Magaji Bichi da Sarkin Musulmi da Shehun Borno da sarakunan Kano da Zazzau da Daura da Lafiya da Rano da Gaya da Karaye da wasu manyan baki da dama ne suka halarci taron.