Bictor Moses ya fara wasa da kafar dama a Turkiyya

Rahotanni daga Turkiyya sun ce tsohon dan kwallon Super Eagles, Bictor Moses ya fara wasa da kafar dama a gasar rukuni-rukuni na Turkiyya inda a karshen makon jiya ya zura kwallonsa ta farko a raga bayan kulob dinsa Fenerbache ya lallasa na Gazisehir Gaziantep da ci 5-0 a wasansu na farko. Rahoton ya ce Moses […]

Bictor Moses ya fara wasa da kafar dama a Turkiyya

Rahotanni daga Turkiyya sun ce tsohon dan kwallon Super Eagles, Bictor Moses ya fara wasa da kafar dama a gasar rukuni-rukuni na Turkiyya inda a karshen makon jiya ya zura kwallonsa ta farko a raga bayan kulob dinsa Fenerbache ya lallasa na Gazisehir Gaziantep da ci 5-0 a wasansu na farko.

Rahoton ya ce Moses ne ya fara zura kwallo a raga a bugun finareti a minti na shida sannan ya taimaka wajen zura kwallo ta biyu a yayin wasan.

Idan za a tuna Moses ya daina buga wa Super Eagles kwallo kuma hakan ya sa bai halarci gasar cin Kofin Afirka da aka yi a bana a Masar.

Ya canja sheka ce daga Ingila zuwa kulob din Fernabache don ci gaba da wasan kwallon kafa.