Biden ya goyi bayan Nijeriya ta samu kujerar dindindin a MDD

Shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana goyon bayansa ga ƙoƙarin Nijeriya na samun kujerar dindindin a Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya. A yayin wata hira ta wayar tarho tsakaninsa da takwaransa na Nijeriya, Bola Tinubu a ranar 29 ga watan Oktoba, Biden ya bayyana aniyar inganta wakilcin nahiyar Afirka a tsarin Majalisar Ɗinkin Duniya. […]

Biden ya goyi bayan Nijeriya ta samu kujerar dindindin a MDD

Shugaban Kasar Amurka, Joe Biden

Shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana goyon bayansa ga ƙoƙarin Nijeriya na samun kujerar dindindin a Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya.

A yayin wata hira ta wayar tarho tsakaninsa da takwaransa na Nijeriya, Bola Tinubu a ranar 29 ga watan Oktoba, Biden ya bayyana aniyar inganta wakilcin nahiyar Afirka a tsarin Majalisar Ɗinkin Duniya.

Ministan Harkokin Wajen Najeriya Yusuf Tuggar, wanda ya yi tsokaci a kan hirar ta tsawon minti 30, ya yi ƙarin haske game da matsayar ta Biden.

“Shugaba Biden ya bayyana ƙarara cewar bai ga dalilin da Nijeriya ba za ta samu kujerar dindindin a kwamitin tsaron Majalisar Ɗinkin Duniya ba,” a cewar Tuggar, inda ya jaddada muhimmancin samun goyon bayan Shugaba Biden.

Tattaunawar ta dace da muhawarar da ake ci gaba da yi game da wakilcin ƙasashen Afirka a Majalisar Ɗinkin Duniyar.

“Amurka na da aniyar ganin Afrika ta samu kujerun dindindin guda biyu a majalisar,” a cewarsa.

Fatan Nijeriya na samun kujerar dindindin na nuna daɗaɗɗiyar buƙatar ƙara samun wakilci a harkokin gudanarwar duniya.

A halin yanzu, Afirka na da kujerun karɓa-karɓa guda uku a Kwamitin Tsaron Majalisar Ɗinkin Duniyar mai mambobi 15, yayin da a duk bayan shekaru biyu babban zauren majalisar ke zaɓar mambobin da ba na dindindin su biyar na wa’adin shekaru bibiyu.