Bidiyon azabtarwa: Gwamnatin Katsina za ta binciki Hisbah

Gwamnatin Katsina ta kafa kwamitin bincike kan zargin da ake wa jami’an Hisbah da azabtar da jama’a

Bidiyon azabtarwa: Gwamnatin Katsina za ta binciki Hisbah

Jami’an Hisbah

Gwamnatin Katsina ta kafa kwamiti da zai binciki zargin da ake wa jami’an hukumar Hisbah na azabtar da jama’a a jihar.

Wannan dai na zuwa ne bayan wani bidiyo da ake zargin jami’an hukumar na azabtar da mutane.

Sakataren gwamnatin jihar, Abdullahi Garba-Faskari, ya ce an dora wa kwamitin alhakin gudanar da binciken sahihancin bidiyon da kuma gaskiyar zargin azabtar da wasu mutane da ake wa jami’an Hisbah.

A cewarsa, an dauki matakin ne bayan rahotanni da korafe-korafe da gwamnati ta samu.

Ya ce mukaddashin gwamnan jihar, Faruk Lawal-Jobe, ya bayar da umarnin a kafa kwamitin da zai binciki zargin tare da bayar da shawarwari.

Garba-Fskari ya bayyana cewa kwamitin zai kasance karkashin jagorancin kwamishinan matasa da wasanni, Aliyu Lawal.

Ya ce mambobin kwamitin sun fito ne daga ma’aikatun harkokin addini, tsaro na cikin gida da shari’a, ma’aikatar kula da ayyukan gwamnati, da kuma hadaddiyar kungiyoyin farar hula (CSOs), yayin da Daraktan Tsaro, ofishin SSG zai zama sakatare.