Bidiyon batsa: Kotu ta ɗaure ’yan Tiktok a gidan yari a Kano
Kotu ta yanke ’yan TikTok ɗin hukuncin ɗaurin shekara guda kowannensu a gidan yari saboda yaɗa bidiyon da bai dace ba

Bidiyon batsa ya ja wa wasu ’yan Tiktok biyu hukuncin ɗaurin shekara guda kowannensu a gidan yari bayan an gurfanar da su gaban kotu a Jihar Kano.
Kotun Majiatare da ke Norman’s Land a Ƙaramar Hukumar Fagge ta yanke wasu ’yan Tiktok din hukunci ne bayan samun su da laifin saɓa wa dokokin Musulunci da kuma tsarin zamantakewar al’ummar jihar.
’Yan TikTok ɗin da suka haɗa da Ahmad Isa da Maryam Musa waɗanda dukansu ’yan unguwar Ladanai ne da ke yankin Hotoro ne.
Sun gurfana a kotu ne bayan da Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta cika hannunta da su.
- Jami’an tsaro sun hana jama’a kwasar mai bayan hatsarin tanka a Taraba
- Yadda Kano ta koma matattarar ’yan TikTok bayan Hisbah ta daina kamensu
- NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Sa Ba Mu Bayar da ‘Ramadan Basket’ Ba
Lauyan Gwamantin Kano, Barista Garzali Maigari Bichi, ya karanta wa matasan takardar tuhumar da ake musu na haɗa baki tare da yaɗa bidiyon da bai dace ba a dandalin sada zumunta, kuma sun amsa laifin.
Daga nan alƙalin kotun, Mai Shari’a Hadiza Muhammad Hassan ta yanke wa kowannensu hukuncin zaman shekara guda a gidan yari.
Ta kuma ba su zaɓin biyan tarar Naira dubu ɗari kowannensu, tare da gargaɗin su da su zama mutanen kirki.