Bidiyon Dala: Kotu ta sanya ranar yanke hukunci kan kama Ganduje

Tsohon gwamnan ya bukaci a dakatar da bincikensa kan bidiyon dala.

Bidiyon Dala: Kotu ta sanya ranar yanke hukunci kan kama Ganduje

Tsohon Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje

Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta tsayar da ranar 22 ga watan Satumba domin yanke hukunci kan bukatar tsohon Gwamnan Jihar, Abdullahi Umar Ganduje ta neman a dakatar shirin kama shi kan faifan bidiyon Dala.

Aminiya ta rawaito cewa, a ranar 7 ga watan Yuli, kotu ta hana Hukumar Karbar Koke-Koke da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar (PCACC) da ‘yan sanda da wasu mutane shida daga gayyata ko kama Ganduje ko iyalansa ko kuma duk wani da ya yi aiki a gwamnatinsa.

Ganduje ya nemi kotu ta ba da umarnin hana hukumar bincikarsa ko kuma gayyatarsa kan bidiyon Dala da ake zarginsa da shi.

A zaman da aka ci gaba a ranar Talata, lauyan wanda ya shigar da kara, Matthew Burkaa (SAN) ya yi karin haske kan martanin wadanda ake kara, inda ya ce babban abin da ya dace shi ne kare hakkin Ganduje sannan kuma ya nemi ya kare iyalansa da kuma masu rike da mukaman siyasa a mulkinsa.

“Ba muna cewa kada a gayyaci Ganduje ko a bincike shi ba ne amma a bi tsarin da doka ta tanada,” in ji shi.

Sai dai lauyan PCACC, Femi Falana (SAN), ya shaida wa kotun cewa kariyar da Ganduje ke da ita ta kare a ranar 29 ga watan Mayu.

W“annan shari’a ta shafi bukatun jama’a ne ba abu ne na bukatar kai da kai ba. Mai shigar da kara na son a yi amfani da doka don kare mutuncinsa da kuma kare bangarorin da ba sa gaban kotu,” in ji shi.

Falana ya ce kotu ba za ta iya kare wadanda ba sa gaban kotun ba.

“Hukumar PCACC ta gayyaci wanda ake zargin don bincike kan badakalar Naira biliyan daga. Don haka idan an gayyace ka dole ne ka girmama gayyatar,” in ji shi.

Ya bukaci kotun da ta yi watsi da bukatar wanda ya shigar da karar.

Tun da fari dai shugaban hukumar, Barista Muhyi Magaji Rimin Gado ya gayyaci tsohon gwamnan don amsa tambayoyi game da bidiyon dala da aka hange shi a ciki.