Bidiyon Janar Rabe a hannun ’yan bindiga ya karya mana zuciya —’Yan uwansa
Iyalan Janar Rabe sun nuna damuwa bayan fitowar bidiyonsa tare da matarsa a hannun masu garkuwa da mutane
’Yan uwan Manjo-Janar Abubakar Rabe mai ritaya sun bayyana damuwa matuƙa bayan kallon bidiyo tsohon babban jami’in sojin tare da matarsa a hannun ’yan bindiga a cikin daji.
Janar Rabe, wanda tsohon Daraktan Yaɗa Labarai na Rundunar Tsaro ne, na kan hanyarsa ta zuwa Jihar Katsina tare da matarsa, Hajiya Amina, da direbansu Abdullahi Sa’idu a ranar 30 ga Mayu, lokacin da wasu ’yan bindiga suka kai musu hari a kan titin Marabar Musawa zuwa Kafinsoli da ke Ƙaramar Hukumar Matazu ta Jihar Katsina.
Lamarin ya faru ne a kusa da ƙauyen Zakin Ɓaure, inda ake zargin ’yan bindiga sun fito daga maɓoyarau, suka tare hanyar tare da buɗe wa motar wuta, lamarin da ya tilasta musu tsayawa.
Majiyoyi sun ce direban ya samu raunin harbin bindiga a hannu yayin harin, amma daga baya maharan suka ƙyale shi.
- Sojoji sun ceto mata da yara 360 da Boko Haram ta sace a Borno
- Kisan mutane 37 a Tureta: Gwamnatin Sakkwato ta ba da tallafin N45m
Wani fitaccen shugaban ’yan bindiga, Muhammadu Kachalla, ya tuntubi iyalan tsohon Janar ɗin bayan faruwar lamarin.
Damuwa kan makomar Janar Rabe da matarsa ta ƙaru ne a ƙarshen mako bayan da masu garkuwar suka saki wani bidiyo da ke nuna Janar Rabe da matarsa a hannunsu.
A cikin bidiyon, an ga ma’auratan tsaye suna isar da saƙon buƙatun masu garkuwar.
Matar Janar ɗin ta ce masu garkuwar na neman a saki wasu mutane uku da gwamnati take tsare da su, waɗanda ta bayyana sunayensu da Sani, Aminu da Nasiru. Ta ce an kama mutum biyu daga cikinsu a Jiƙamshi, yayin da aka kama na ukun a Kano.
Haka kuma masu garkuwar sun buƙaci a mayar musu da dabbobin da suka ce jami’an tsaro sun ƙwace a lokacin wani samame da aka gudanar a kasuwar Jiƙamshi da ke Ƙaramar Hukumar Musawa.
Matar Janar Rabe ta yi kira ga gwamnatin Jihar Katsina da shugabannin ƙananan hukumomi biyar da su taimaka wajen cika waɗannan buƙatu domin samun ’yancinsu.
Shi ma Janar Rabe, wanda ya yi gajeriyar magana a cikin bidiyon, ya yi kira da a ƙara ƙoƙarin samar da zaman lafiya, yana mai cewa masu garkuwar sun nuna sha’awar tattaunawa da zaman lafiya.
“Sun bayyana mana irin ƙoƙarin da suke yi wajen kare yankin da tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa. Amma daga baya sun nuna rashin gamsuwa da yadda hukumomin yankin suka yi. Ina ganin gwamnati ya kamata ta koma tattaunawa da waɗannan mutane domin dawo da zaman lafiya mai ɗorewa,” in ji shi.
An lura cewa ma’auratan sun bayyana cikin nutsuwa a cikin bidiyon, ba tare da wasu alamun cin zarafi ko azabtarwa a jikinsu ba.
“Bidiyon ya karya mana zuciya”
Da take bayani kan bidiyo, a cikin hawaye, Mariya Ibrahim, ƙanwar Janar Rabe, ta ce iyalan sun shiga matsananciyar damuwa bayan kallon bidiyon.
“Da muka gan shi tare da matarsa a wannan hali, gaba ɗaya mun kasa daurewa. Wannan ɗan uwanmu ne da ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa ƙasar nan hidima. Muna roƙon gwamnati ta ɗauki mataki cikin gaggawa kafin lokaci ya kure,” in ji ta.
Wani ɗan uwa kuma na kusa da iyalan, Ibrahim Mamman Batsari, ya ce bidiyon ya jefa iyalan cikin matsananciyar damuwa.
“Ba wai garkuwa da mutane kaɗai aka yi ba, an kuma azabtar da mu ta fuskar tunani. Ganin sa a cikin wannan hali ya girgiza mu ƙwarai. Dole gwamnati ta ɗauki mataki yanzu, ba sai gobe ba,” in ji shi.
Ita ma A’isha Abubakar Batsari, wata ƙanwar Janar Rabe, ta ce tun bayan fitowar bidiyon iyalan suka rasa sukuni.
“Ba ma iya barci. Duk lokacin da muka rufe idanunmu, wannan bidiyon ne ke dawo mana. Muna cikin damuwa kan lafiyarsu da tsaron rayuwarsu,” in ji ta.
Wasu ƙannensa biyu, Abubakar Barau Batsari da Hamisu Abubakar Batsari, sun bayyana bidiyon a matsayin abin da ya jefa danginsu cikin firgici da tashin hankali.
“Tun bayan kallon bidiyon muke ta kuka. Ya girgiza mu matuƙar. Muna roƙon Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin Jihar Katsina, tare da dukkan hukumomin tsaro, su ceto su cikin ƙoshin lafiya ba tare da wata illa ba,” in ji Hamisu.
Shi kuwa Abubakar ya ce: “Duk wani jinkiri da ka yi akwai ƙarin haɗari. Muna roƙon hukumomi su ɗauki wannan batu a matsayin lamarin gaggawa.
Al’ummar Batsari sun shiga tashin hankali
Sace Manjo Janar Abubakar Rabe da matarsa ya ci gaba da haifar da fargaba da damuwa a tsakanin mazauna Batsari da sauran al’ummomin da ke maƙwabtaka da yankin.
Wani jagoran al’umma a yankin, Alhaji Haruna Mai Maganin Kwari Batsari, ya ce bidiyon da masu garkuwa suka fitar ya ƙara tsoratar da jama’a.
“Mutane sun shiga fargaba. Idan har za a iya sace tsohon Manjo Janar da matarsa sannan a ɗauki bidiyonsu a wannan hali, to talakawa sun fi kasancewa cikin haɗari,” in ji shi.
Wani masanin harkokin tsaro da ke zaune a Katsina, Abubakar Ibrahim, ya bayyana bidiyon a matsayin wata alama ta ƙalubalen tsaro da ƙasar ke fuskanta.
“Wannan bidiyo ya nuna irin ƙarfin halin da ƙungiyoyin masu aikata laifuka suka samu.
“Abu ne mai sosa rai a ga wani tsohon babban jami’in soja a irin wannan hali na rashin galihu. Wannan na aika da saƙo mai haɗari game da halin da tsaron ƙasa yake ciki,” in ji shi.
Don haka ya buƙaci hukumomin tsaro da su sake nazarin dabarunsu cikin gaggawa.
“Ya kamata wannan lamari ya sa a sake duba yadda ake tattara bayanan sirri, saurin mayar da martani da kuma shirye-shiryen gudanar da ayyuka.
Ya ƙara da cewa “Dole ne gwamnatin ƙasa ta nuna cewa tana iya kare ’yan ƙasarta, musamman waɗanda suka sadaukar da rayuwarsu wajen kare ta.”