Bidiyon tsaraicin Maryam Booth bai shafi kungiyarmu ba – Alhasan Kwalle

Bullar bidiyon tsiraici na fitacciyar jarumar fina-finan Hausa Maryam Booth a makon jiya ya jawo maganganu a kan wadanda suka saki bidiyon da dalilan sakin bidiyon. Wadansu na ganin cewa makiyan jarumar ce suka saki bidiyon don tozarta ta, yayin da  wadansu ke ganin tsohon saurayin jarumar da ake zargi da saki bidiyon, ya yi […]

Bidiyon tsaraicin Maryam Booth bai shafi kungiyarmu ba – Alhasan Kwalle

Bullar bidiyon tsiraici na fitacciyar jarumar fina-finan Hausa Maryam Booth a makon jiya ya jawo maganganu a kan wadanda suka saki bidiyon da dalilan sakin bidiyon. Wadansu na ganin cewa makiyan jarumar ce suka saki bidiyon don tozarta ta, yayin da  wadansu ke ganin tsohon saurayin jarumar da ake zargi da saki bidiyon, ya yi haka ne bayan dangantaka a tsakaninsu ta yi tsami.

A cikin bidiyon dai mai tsawon dakika uku an ga jaruma Maryam Booth tsirara haihuwar uwarta, inda cikin sauri ta taho tana kokarin karbe wayar daga hannun mai daukar bidiyon nata.

Da Aminiya ta tuntubi Shugaban Kungiyar ’Yan Wasa ta Kannywood, Alhassan Kwalle, ya ce bullar wanann bidiyo bai shafi kungiyarsu ba, lura da cewa abin ya shafi rayuwarta ta zahiri ce ba wai ta fim ba.

“A gaskiya duk da cewa wannan yarinya tana cikin mu ’yan fim amma wannan abu bai shafi kungiyarmu ta fim ba, abu ne da ya shafi rayuwarta. A gida ne ta yi abinta ba wai a wajen fim ba. Don haka kungiyarmu babu wani mataki da za ta dauka a kanta kuma abin bai shafe mu ba,” inji shugaban.

A cewar Alhassan Kwalle, mutumin da ya saki bidiyon tsiraicin jarumar ya yi ne don tozarta ta tare da cin mutuncinta, lura da cewa an dauki tsawon lokaci da daukar bidiyon amma ba a sake shi ba sai a wannan lokaci.

“Wannan bidiyo ba yanzu aka dauke shi ba. An ce an kai kimanin shekara uku da daukarsa. Duk wanda ya saki bidiyon ya yi shi ne don ya ci mutuncinta, domin an dade ana karbar kudi a hannunta tare da yi mata barazanar sakin bidiyon. A wannan lokaci mutumin ya nemi kudi a hannunta wai zai kai mahaifiyarsa asibiti, da ba ta ba shi kudin ba ne, sai ya yi amfani da wannan dama ya yi abin da ya yi,” inji Kwalle.

Ya ce, “Ina mamakin yadda ake sanya wa ’yan fim ido, domin kafin bayyanar wanann bidiyo an samu na wadansu mutane da suka fi, bidiyon makamancin wannan amma ba a yi irin wannan babatun ba.”

A cewar Alhassan Kwalle, a yanzu haka maganar tana gaban jami’an tsaro domin binciko  masu hannu a cikin lamarin tare da daukar matakin da ya kamata. “Yanzu magana tana gaban hukuma, za a binciko wadanda ke da hannu a cikin sakin bidiyon. Domin tun farko ta yi niyyar daukar mataki a kan lamarin sai aka ba ta hakuri, aka kuma tabbatar cewa an goge bidyon amma sai ga shi daga baya an sake shi.

“A yanzu haka akwai mutum biyu da ake zargi da sakin bidiyon, wadanda kuma dukkansu ba ’yan fim ba ne. Zai iya yiwuwa wanda ya dauki bidiyon ne ya sake shi ko kuma wanda aka ba shi daga baya, shi ya saki wannan abu. Da zarar jami’an tsaro sun kammala bincike za mu sanar da jama’a halin da ake ciki,” inji shi.

Bayan bullar bidiyon, wadansu jarumai mata na masana’anatar sun yi surutai cewa bidiyon na jaruma Maryam ba ya da wani muni kuma wai a cewarsu wani abu ne kankane. Da Aminiya ta tambayi Alhasan Kwalle kan wadannan kalamai nasu ba nuni suke ga irin zargin da aka dade ana yi kan jarumai mata, cewa ’yan iska ne, sai ya ce,. “Abin da nake so ki gane shi ne, zargi ba za a daina yi wa ’yan fim ba. Ko malami ne ba ya wuce zargin mutane ballantana mu ’yan fim. Kowa yana da ra’ayinsa, don haka wancan ra’ayi nasu ne ba na dukkan ’yan fim ba.”

Sai ya ce, “Ina kira ga kungiyoyin kare hakkin mata su dauki mataki don dakile irin wannan cin mutunci da ake yi wa ’ya’ya mata a kafafen sada zumunta na zamani. Bai kamata a ce ana ci gaba da zura idanu maza suna cin mutuncin mata ta irin wannan siga, ba tare da daukar mataki a kansu ba.”

Isma’ila Na’abba Afakallah shi ne Shugaban Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano, ya bayyana cewa hukumarsu ba ta da wani hurumi kan batun bidiyon, lura da cewa hukumarsu tana aiki ne kan abin da ya shafi fim ba dan fim ba.

“A gaskiya aikinmu shi ne mu duba tare da tace duk wani abu da aka dauka da sunan fim, wanda  za a yada shi don jama’a su gani. Amma irin wannan bai shafe mu ba, duk kuwa da kasancewar yarinyar ’yar fim ce,” inji shi.

Limamin Masallacin Juma’a na Triumph da ke Kano, Malam Lawal Abubakar ya shaidawa Aminiya cewa daukar bidiyon tsiraici da yada shi a tsakanin mutane haramun ne a Musulunci.

“Addinin Musulunci bai yarda mutum ya zauna tsirara wani ya ga tsiraicinsa har ya dauki hotonsa ko kuma shi da kansa ya duki hoton tsiraicinsa ba. Haka bai yarda da yada alfasha ba. Allah Ya yi hani da aikata alfasha da kuma yada ta. Idan aka samu mutum yana bayyana laifi, alama ce ta kaiwa karshe a  aikata laifi. Manzon Allah (SAW) ya ce duk al’ummarsa idan suka yi laifi Allah Yana yafe musu amma ban da wadanda suke bayyana laifi. A takaice abu ne mara kyau a addinance,” inji shi.

Malam Lawal ya kara da cewa: “Abin bakin ciki ne a ce ’ya’yan Musulmi ne ke aikata haka. Wannan yana nuni da irin kaiwa matuka ta lalacewar tarbiyyar al’umma. Sai dai mu sani cewa fitar bidiyon zai iya zama wata hanya ta wa’azi ga ita wacce ke jikin bidiyon da sauran masu aikata irin laifinta, domin hakan zai iya zama sanadin yin nadamarta, sannan a waje daya ya zama izina ga wadanda ke aikata makamancin haka a boye su tuba, su daina. Allah (SWT) Yana karbar tubar bawanSa matukar bawan bai guji Allah ba.”

Malamin ya ce “Akwai bukatar hukuma ta yi doka a kan iri wannan. Akwai abubuwan da wa’azi kadai ba ya aiki a kai. Shi ya sa bayan Allah Ya saukar da wa’azi a gefe guda kuma Ya saukar da haddi. Akwai mutanen da wa’azi kadai ba ya yi musu tasiri amma idan suka san za a dauki wani mataki a kansu, to za su shiga taitayinsu gudun abin da zai faru gare su,” inji shi.

Maryam Booth ta wallafa a shafinta na Twitter, cikin Ingilishi cewa: “Ina sane da halin da ake ciki a kafafen watsa labarai game da bidiyon da ya fita, wanda ni ce a jiki, kuma kafafen watsa labarai, musamman na sada zumunta suka watsa shi; wanda zuwa yanzu dubban mutane suka kalle shi. Da farko na so in yi shiru har sai jami’an tsaro su kammala bincikensu amma sai kalamin wani Ibrahim Ahmad Rufa’i (Deezel) ya sanya dole in yi magana. A matsayina na mace kuma ’yar fim, wacce wadansu ke koyi da ita ba zan bar wannan magana ta shashance a haka ba.”

Jarumar ta ci gaba da cewa: “Ina so in fito in bayyana cewa shi wannan mutum Ahmad Rufa’i ya sha yi min barazanar zai fitar da wannan bidiyo idan ban ba shi kudi ba. A matsayina na mace kuma ’yar fim a bar kwaiwayo ga miliyoyin mutane, na yi ta kokarin kare mutuncina iya yadda zan iya, amma sai ga shi bidiyon da aka dauka shekara uku da suka wuce an sake shi. A lokaci irin wannan mutum ya kamata ya yi taka-tsantsan kafin yin magana amma gaskiya ce Deezel tsohon saurayina ne wanda ya dauki bidiyon, lokacin da nake canja kaya. A yanzu ina tattauanwa da duk makusantana da mashawartana game da yiyuwar daukar matakin shari’a a kan duk wanda ke da hannu a kan fitar da hoton bidiyon,” inji shi.

A karshe Maryam ta yi godiya ga ’yan uwanta da masoyanta, inda ta ce: “Ina gode wa ’yan uwana da kawayena, musamman masoyana game da damuwa da tausaya min da suka yi a wannan lokaci na jarrabawa. Na gode muku.”

A nasa bangaren, wanda jarumar ke zargi, Ibrahim Ahmad Rufai wanda ake fi sani da Deezel ya musanta zargin da take masa, inda ya ce ba ya da masaniya kan faifan bidiyon.

Deezel ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter, inda ya ce, “Ina so in bayyana wa duniya cewa ban taba ce wa Maryam Booth ta ba ni kudi ko in saki wani faifan bidiyonta ba.

“Ban taba nadar bidiyon Maryam a labe ba, lokacin da take canja kaya kuma ban san wanda ya nadi bidiyon ba.”

Ya kara da cewa yana bukatar Maryam ta janye zargin da take masa cikin sauri, “Ina so ta yi gaggawar janye zargin da take mini, sannan ta nemi afuwa a kafafen sadarwa na zamani inda ta yada zargin.”

Ya ce ya riga ya yi shawara da lauyoyinsa kan batun, sannan kuma sun riga sun ba shi shawarar abin da ya kamata ya yi.

 

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50