Bidiyon Tsiraici: Hafsat Baby ba ta hannunmu —Hisbah

Hisbah ta bayyana dalilin da Sheikh Daurawa ya goge bidiyon da ya wallafa

Bidiyon Tsiraici: Hafsat Baby ba ta hannunmu —Hisbah

Jami’an Hisbah

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta bayyana cewa ba ta kama jarumar TikTok Hafsat Baby wadda ake nema kan bidyon tsiraicinta ta ya karaɗe kafofin sada zumunta ba.

Hakan na zuwa ne bayan a ranar Litinin Babban Kwamandan hukumar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya wallafa wani bidiyo da cewa jami’ansu sun kama jarumar TikTok ɗin da ta yi bidiyon tsiraici.

Amma cikin ƙasa da awa biyu ya goge bidiyon daga shafinsa na Facebook, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce.

Amma Babban Daraktan hukumar, Abba Sa’id Sufi, ya shaida wa Aminiya cewa har yanzu Hisbah ba ta kama Hafsat din ba.

Abba Sa’id Sufi ya ce amma hukumar ta baza jami’anta ko’ina domin farautar Hafsat Baby da sauran waɗanda suke aikata baɗala a kafar ta TikTok.

Ko da ka tambaye shi game da bidiyon da Sheikh Daurawa ya wallafa, Abba Sufi ya bayyana cewa wadda aka nuna a cikin bidiyon ba ita ce Hafsat Baby, wata ce ’yar lukuta da suke kama hukumar ta kama.

Ya ci gaba da cewa wannan ne ya sanya aka sauke bidiyon da aka wallafa.

Sannan ya ƙara da cewa hukumar ta baza komarta domin kama duk waɗanda suke da hannu wajen yin wannan bidiyon na bayyana tsiraici.

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara

Ɗan shekara 60 ya rasu bayan faɗawa a rijiya a Kano