Bidiyon tsiraici ya janyo cire jaruma daga fim din Kwana Casa’in

Ita dai Safara’u a cikin fim din an nuna yarinya ce mai natsuwa mai son karatu wacce ke burin ta zama likita.

Bidiyon tsiraici ya janyo cire jaruma daga fim din Kwana Casa’in

Safara’u ta cikin shirin Kwana Casa’in

Ga masu kallon wasan kwaikwayon nan mai dogon zango na Kwana Casa’in da tashar tauraron dan Adam ta Arewa 24 ke nunawa sun wayi gari da ganin wata sabuwar fuska da ta maye gurbin jarumar da take fitowa a matsayin Safara’u a cikin fim din, wanda hakan ya janyo ’yan kallo masu yawa suka shiga neman bayanin dalilin da ya kawo wannan canji da aka samu.

Safara’u a cikin fim din

Ita dai Safara’u a cikin fim din an nuna yarinya ce mai natsuwa mai son karatu wacce ke burin ta zama likita.

Ana nuna ta a matsayin yarinya da babu ruwanta da shashanci. Kuma duk da cewa iyayenta talakawa ne ba ta da kwadayi ko son mallakar abin
duniya kamar yadda wadansu ’yan matan ke yi.

Hakan ya janyo ta zama tauraruwa babba, kuma abar so da ’yan kallo masu yawa ke matukar so.

Abin da ya sa aka canja ta

Binciken Aminiya ya gano cewa Hukumar Gidan Talabijin na Arewa 24 ta canja jarumar wadda asalin sunanta Safiyya Yusuf ce da wata mai suna Maimuna Musa sakamakon bullar wani bidiyon tsiraici na jarumar a kwanakin baya wanda ake zargin ta aike wa saurayinta wanda daga baya ya shiga hannun jama’a ya jawo cece-ku-ce.

Aminiya ta nemi tattaunawa da Gidan Talabijin na Arewa 24 inda suka ki cewa komai kan batun, sai dai wata majiya mai tushe ta tabbatar da cewa canjin ’yar wasan ya samu ne sakamakon bullar bidiyon tsiraici da ake zargin jaruma Safiyya Yusuf da shi wanda kuma zai iya shafar fim din kai-tsaye.

“Kin san kwanakin baya an samu wani bidyon tsiraici na jarumar wanda kuma aka yi ta yada shi a kafafen sada zumunta na zamani hakan ya janyo aka yi ta sukar yarinyar tare da jan hanaklin Hukumar Gidan Talabijin na Arewa 24 kan su dauki wani mataki domin abin nata zai iya shafar gidan kai-tsaye. Ta yadda ake tunanin mutane ma za su iya kaurace wa kallon fim din wanda yake da dimbin masu kallo. Hakan ya sa wannan gidan talabijin ya dauki wannan mataki don neman rike masu kallon wannan shiri,” inji majiyar.

Wata majiyar ta ce ko ba badakala ana iya canja jarumi ko jaruma a tsarin fim mai dogon zango, inda ta ce ko a fim din Dadin Kowa hakan ya faru haka sauran fina-finai na duniya masu dogon zango, inda akan iya canja jarumi.

Na ji daban da aka canja ta – Bashir Nayaya

Da yake yi wa Aminiya bayani kan yadda ya ji, dan wasa Bashir
Nayaya da ke fitowa a matsayin mahaifin Safara’u ya ce duk da cewa shi dan wasa ne da zai iya yin aiki da kowane dan wasa dan uwansa amma ya bayyana sauyin da cewa ya shafi gudanar da wasan.

“To kin san ko da ne idan ka saba aikensa sayen wani abu to duk ranar da ka aiki wani dan daga cikin ’ya’yanka sai ka ga bambanci. Ita waccan yarinya da ita muka fara mun saba muna gudanar da shirin tare. Da zarar an dora mana kyamara mun san abin da za mu yi wanda kuma zai
burge dan kallo. Amma kin ga ita wannan sabuwa ce yanzu aka fara
da ita, to ai ba za ki hada ba. Sai dai ita ma a hankali za ta saba da yin abin da ake so,” inji shi.

Abin da masu kallo suke cewa
Yawancin masu kallon fim din na Kwana Casa’in ba su ji dadin
sauyin da aka samu ba, saboda a cewarsu jarumar tana yin iya
kokarinta a matsayin da aka ba ta a cikin fim din kamar yadda suka shaida wa Aminiya.

Malam Kabiru Usaini ya ce bai ji dadin canjin da aka samu ba domin wacce aka canja a matsayin nata ba ta yin abin kamar na Safara’un ta baya.

“A gaskiyaban ji daxin canjin ba, domin ita wannan Safara’un da
aka sanya ba ta yin abin kamar waccan Safra’un,” inji shi.

Ita ma Zainab Sani cewa ta yi canja Safra’un da aka yi a fim din bai yi musu daxi ba saboda Safra’un farko tana yin wasanta da gaske.

“Matsalar da aka samu ita Safarau ta farko ta fi iya aikin, ga shi kuma tana da siffar tausayi. Amma ita wannan kana kallon ta tana yin abin kamar a fim ba na gaskiya ba.”

Duk kokarin Aminiya don jin ta bakin jaruma Safiyya Yusuf ya ci tura saboda ba ta iya samunta a wayarta ta hannu ba.

Waiwaye
Idan ba a manta ba, a kwanaki an samu irin wannan lamarin, inda aka samu bullar wani faifan bidiyo na jarumar Kannywood, Maryam Booth, wanda a lokacin aka zargi wani tsohon saurayinta, Deezel da fitarwa, duk da cewa ya musanta zargin.

Bidiyon a wancan lokaci ya tayar da kura matuka, inda daga karshe aka garzaya kotu, Maryam tana neman hakkinta bisa zargin bata mata suna, shi kuma yana musanta zargin tare da cewa shi ma an bata masa suna ta hanyar sanya sunansa a cikin lamarin.

Aminiya ta ruwaito yadda mahukunta da jarumai manya
da kanana a Masana’antar Kannywood suka yi kokari matuka wajen tare wa Maryam fadan, inda har wadansu mahukunta suka nuna cewa lamarin bai shafi fim ba, don haka ba za a dakatar da ita daga shirin fim ba.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya