Bidiyoyin da suka ɗauki hankalin ’yan Najeriya a 2024

Bidiyon faɗuwar Shugaban Ƙasa Bola Tinubu a bikin Ranar Dimokuraɗiyya na daga cikin jerin bidiyoyin da suka fi ɗaukar hankali a 2024

Bidiyoyin da suka ɗauki hankalin ’yan Najeriya a 2024

Gwamnan Kano Abba da Sheikh Daurawa

A yayin da shekarar 2024 ta zo gangara, Aminiya ta yi nazari tare da rairayo maku wasu bidiyoyin da suka ɗauki hankalin ’yan Najeriya a shekara.

Waɗannan bidiyoyi sun haɗar da na murabus ɗin Kwamandan Hisbah na Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa; faduwar Shugaba Tinubu a wurin taron bikin Ranar Dimokuraɗiyya da dai sauransu.

1- Tsegumin sojan kan yaƙi da ’yan ta’adda:

A shekarar bidiyon wani soja ya karaɗe kafofin sada zumunta inda q ciki yake bayyana wasu muhimman matsalolin yaki da ’yan ta’adda a Najeriya. Sojan ya yi zargi cewa akwai wasu manyan mutane da ba sa son Najeriya ta zauna lafiya, shi ya sa suke hana sojoji damar yin aiki yadda ya kamata don kawo ƙarshen ta’addanci a ƙasar.

Sojan ya ce akwai isassun kayan aiki a hannun sojojin Najeriya, fiye da na ’yan ta’adda inganci da fasaha, yana mai cewa idan aka ba su umarnin da ya dace, za su iya gamawa da duk wasu ’yan ta’adda a cikin sati daya zuwa biyu kacal.

Wannan bidiyo ya ja hankalin al’umma matuƙa musamman bayan samun rahoton cewa Hukumar Sojin Najeriya ta ɗauki matakin hukunta wannan jami’in nata a kan bidiyon, da kuma yawan kiraye-kirayen al’umma na neman a yi gyara a tsarin yaƙi da ta’addanci a Najeriya.

2- Faɗuwar Tinubu a Ranar Dimokuraɗiyya:

A Ranar Dimokuraɗiyyar wannan shekara da muke bankwana da ita, an ga yadda Shugaba Tinubu ya zame bayan ya rasa wurin ɗora ƙafa a yayin hawa motar da za ta zagaya da shi dandalin Eagles Square. Sai dai jami’an tsaronsa sun tallafa masa ya miƙe.

Wannan lamari ya ja hankalin ’yan qasar suka yi ta tofa albarkacin bakinsu musamman a shafukan sada zumunta, inda wasu suka jajantawa shugaban ƙasar mai shekara 72, wasu kuma suka riƙa tsokanar shi.

Sai dai a martanin da Shugaban ƙasar ya mayar cikin raha, ya ce ba faɗuwar ya yi ba, rusunawa ce ya yi don murnar Ranar Dimokuraɗiyya ta Shekarar 2024. Ya yi hakan ta wani salon gaisuwa inda ake kwantawa a kasa wadda ake kira “dobale” da harshen yarabanci.

3- Waƙar Fatima Mai Zogale:

Waƙar da fitaccen mawaƙin siyasa Dauda Kahutu Rarara ya yi wa wata Fatima mai sana’ar sayar da zogale a Abuja ya karaɗe tattaunawar shafukan sada zumunta a wannan shekara shekara musamman a tsakanin watan Afrilu zuwa Mayu

Waƙar Fatima Mai Zogale ta ja hankalin al’umma musamman bayan fitar bidiyon cewa uwar gidan Fatima ta sallame ta saboda rashin ambaton ta a waƙar. Sakamakon haka, Rarara ya yi alƙawarin taimaka wa Fatima, inda daga bisani mawaƙin ya haɗa wani gangami na mutane suna cin zogale da zummar taimakon Fati.

Rarara ya saki tallar waƙar Fatima Mai Zogala ne a cikin ƙarshen watan huɗu na shekarar 2024, inda ya saki cikakkiyar waƙar a farkon watan biyar na shekarar.

Mutane sun ƙaunaci waƙar wasu domin tausayawa Fatima bisa korar ta da uwar dakinta ta yi, wasu kuma don ganin a karon farko mawaƙin ya yi waƙa ga talaka (mai sana’a) wasu kuma saboda ƙaunar mawaƙin da kuma kasancewar ba kasafai yake waƙoƙin da ba na siyasa ba.

Saboda haka aka yi ta hawa waƙar, a kwana biyu ta karaɗe Arewacin Najeriya kamar yadda wasu masana al’ada suka bayyana.

4- Murabus ɗin Daurawa daga Hisbah:

A safiyar Juma’a 1 ga watan Maris na shekarar 2024 ne, Babban Kwamandan Hisbah na Jihar Kano, Sheikh Aminu Daurawa ya bayyana ajiye aikinsa ta wani bidiyo da ya dora a shafinsa na Facebook bayan zargin rashin samun goyon baya wajen gudanar da ayyukan kawar a baɗala daga mahukunta a jihar.

Sheikh Daurawa ya miƙa murabus ɗin nasa ne ƙasa da sa’o’i ishirin da huɗu bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi wa tsarin samame a kan wuraren baɗala da hukumar Hisbah ta ɓullo da shi da kama masu laifuka ba tare da kima da kiyaye yancin ’yan Adam ba.

Bidiyo da malamin ya saki a lokacin da yake Kaduna, inda suke tattaunawa da ’yan majalisa domin lalubo hanyar sanya dokar gudanar da gwaji na lafiya kafin aure, ya ja hankali a kafofin sada zumunta inda Sai dai shehin malamin daga baya ya ce gwamnati ta ƙi karɓar takardar murabus ɗinsa, kuma sun fahimci juna, ya ci gaba da aikinsa kamar yadda ya saba.