Bikin Bala na Atine

Ranar sili da tsayuwa bisa kafa daya ga watan Farin-birin na kowace shekarar Turawan da ke amfani da tsarin lissafin kwanakin Girgori, ke warwasawa su fantama, su hole a tsakanin samari da ’yan matan duniya. Don murnar bikin Balan-tine ko kuma a yaren Hau-hau wajen hawan sa ba tare da sa-in-sa ba, sai mu kira […]

Bikin Bala na Atine

Generated by IJG JPEG Library

Ranar sili da tsayuwa bisa kafa daya ga watan Farin-birin na kowace shekarar Turawan da ke amfani da tsarin lissafin kwanakin Girgori, ke warwasawa su fantama, su hole a tsakanin samari da ’yan matan duniya. Don murnar bikin Balan-tine ko kuma a yaren Hau-hau wajen hawan sa ba tare da sa-in-sa ba, sai mu kira shi da Bikin Bala na Atine. Kamar yadda jhna taba yin tsokaci a darasin wannan farfajiya, ranar Bikin Balan-tine, ranar tafiya Tunusiya ce, inda zukata ke soyewa, musamman a tsakanin ’yan uwanmu masu addu’a da gicciye; kodayake akwai limamansu da suke adawa da wannan biki, don ganin yadda ’yan bana bakwai suka dagula al’amura, suka mayar da bikin sheke aya.
A wannan babbar rana dai masu jakadun sheke aya za su yi “Rahi ma raha,’ wato a yi tar aha a bariki da ’yar raha.’ kadangarun bariki kuwa da mage da wuri da su dan hamsin, a wannan rana su ne kirazan biki. Lallai Haurobiyawa kowa ya shiga taitayinsa, irin wannan biki bia dace da al’adunmu ba, hasali ma wadanda ke yin limbu-limbu a cikin lambu, su zama ’yan kabu-kabu, domin ba su tanadi komai a a cikin rumbu ba.
’Yan makarantarmu, ganin irin tabargazar da ake tafakwa a ranar bikin Bala na Atine, ya san a ga ya dace in jefa kalubale ga masu wasan Samson siya-siya da kwakwalen al’ummar Haurobiya, da su daina yi mana tatsuhiyar gizo da koki, su daina satar akwati da runton kujera tun kafin tsinuwa ta kama su. Tsinuwar kuwa ita ce, “Allah tsine barawon akwatu haka ma mai runton kujera.” barawon akwatun kuri’ar Haurobiyawa babu wata soyayya da kauna da yake nuna wa al’umma, illa dai kawai ya saci dukiyarsu, ya tafi bariki, ya nmi ‘yar raha su yi ta raha a cikin watan Farin-biri.
Haurobiyawa ina fatan ba za ku shagala da bikin Bala na Atine ba, alhali Gwamnatin kasar Haurobiya ta janye muku duk wani tallafi saukaka radadin halin ha’ula’i a cikin wannan rayuwa. Bisa la’akari da zullumin zalunci shagabannin Haurobiya ya kamata Haurobiyawa su yi ta rusa kuka, maimakon shagalin biki a ranar Bikin Bala na Atine; a ma iya yi masa lakabi da bakin cikin Balbalin bala’i na tunane-tunane.
Inda za kusan cewa ba mu da lokacin bikin sharholiya irin na Balan-tine, shi ne, kasar babu tsaro, sai tsoro. Kowa ya san a cikin darassan wannan makaranta mun taba bijiro da batun jihohi sili da manuniyar sama da kasar Amurka ta yi has ashen babu a tsaro a cikinsu. Don gudun kada cici ya cutar da mutanen kwasarta da ke kai kawo a Haurobiya, sai aka ce su kiyayi wadannan jihohi, wadanda suka ahda da Yawon-Bebe da Birnin Dikko da Dabo da Alan-guburo da wasu a yankin Hauren Danja. Idan har akwai shugaban Haurobiya da ke nuna soyayyar soyewar zukata da kaunar talakawa, to ya yi fafutikar tabbatar da tsaro a wadannan jihohi.
Wani dalili da zai sanya mu kara kaurace wa bikin Balan-tine, shi ne. Asararren Dokin-Bobo da ya sha alwashin zubar da jinin Haurobiyawa matukar Shugaban Gudun-loko bai zarce da mulkin mulka’un jam’iyya mai dan boto da sanda jirge ba.
Shi ma Kansakalin-kuku, ya yi alkawarin tayar da zaune tsaye, a gaban jiga-jigan Hukumar Amurkawa, mutanen Uban-mama, Jikan Kenyawa, Jagoran Amurkawa, cewa matukar Mai Gudun-loko bai ci gaba da jan ragamar Haurobiya a shekara ta dubu karamin lauje da sili da babban lauje, to babu sauran lulumin lumana a yankin Hauren-Danja.
Kai ina ganin dai ranar bikin Balan-tine, ran ace ta son rai ga shagabannin Haurobiya, domin a jerin jiga-jigan gwamnati akwai wadanda suka daure wa jaba da gafiya da kusu kugu, su yi ta cin durwansu babu babbaka. Na sha nanata muku irin wadakar da In-gwangwaje-in-wala da Mace-da-zane da Santala kwaiduwa ke ta duma wasoso a dukiyar al’umma. Kwanan mnan Masanin Sisi-da-sisi ya shiga yamutsi tsakaninsa da jiga-jigan Kamfanin Man tunkuzar kasar Haurobiya, inda bin kadin inda Dalar Hauron Haurobiya Gashin Balama karamin lauje da zagaye ya zuganye.
Ba tare da na cika ku da surutu rututu ba, kamar Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters, ina ganin kiyayyar al’umma ta sanya Baffan-rawa na birnin Mujadaddi ya yi tsallen badaske zuwa jam’iyya mai dan boto da sanda jirge, da nufin jirga al’umma, ya karbo damin Hauro. Shi ma abokin balaguronsa, Malam Iro Shekararren Jihar Tumbin-giwa ya garzaya don kada a yi masa wa ka ci, ka ta shi.
Inda za a fasko cewa bai kamat amu rika holewa a watan Farin-biri ba, shi ne, Gwamna Mai Kwaran-kwatsintsiya na birnin Dabo ya turke dimbin zawarawa a turken ma’aurata, ba tare da ya bari an yi tsarunce ba. ‘’Yan makaranta ya kamata ku gano cewa ni ban zauna a azure ba, domin in yi ta zaurance. Irin wannan dabi’a ai sai mutanen Ka-zauna-a-zaure, ka yi ta zaurance, can a Jihar jijjiga Ciyawa garin Gwamna mai sunan sulalla, wanda ya kasa ficewa daga jam’iyya mai dan boto da sanda jirge, duk da cewa yana da masaniya kan yadda aka shafe shekara sili da tsayuwa bisa kafa daya ana jirga Haurobiyawa. Abokan balaguronsa wajen adawa da gudun-loko sun sama wa kawunansu mafita. Wadannan sum ne masu kaunar al’ummarsu.
Haurobiyawa a yi kokarin bambancewa tsakanin tsaba da tsakuwa; ku yi kopwarin sanin masoyanku, tun daga watan Janye-wuri, har zuwa watan Dashen-Baba, wato farko da karshen kowace shekara ke nan.
Lallai ya kamata Arewatawa su daina dura wa Shekararren mutumin nan ashariya das hi da Baffan-rawa, tunda ba su kadai ne, suka tafi laluben na-koko ba; ga tsoho Tanko Ya-kasa, shi ma ya je ya karbi kasonsa. Babbar manufar wadannan miyagun mutane it ace. Su maisheku ‘Bakaken birai,’ su kuma sun zama “Fararen-Birai,” don haka sai su yi ta sharholiyarsu a cikin watan Farin-biri, inda a kowace ranar sili da tsayuwa bisa kafa daya za su rika yin rahi ma raha da ’yar raha a bariki tare da babban jakadan sheke aya, Akuyar-maman-Daudu, mataimakin Dauda mai maki. Haurobiyawa sai mu nisanci bikin Balan-tine, mu nemi tsarin Mai-duka da miyagun manyan kwabo. Idajn kun ji gargadina, sai in dan tsahirta mu yi fafutika tare da ku, idan kuwa kun kiya, ba ni da mafita, illa in dare bisa kan amale, in arce zuwa birnin Tagas, ni ma in samu bagas.