Bikin balaguron Baba

Du’a’inmu ya samu ijabaUbangiji Ya dubi BabaAllah ya kara masa muhibbaMun nemi kariyar UkubaMun nemi tsarin azaba Salatina ga Annabi mai sahabaAlfarmar dakin  Ka’abaSanya mu daina gabaAnnabi ya yi yarjejniyar AkabaAllahu ya yi hani da giba Baba ya yi balaguroLaulayi ya gangaroBokan-Turai ya tunkaroAllurai aka tsikaroJikin Baba ne aka gyaro Ya yi fama da jinyaDattijo […]

Bikin balaguron Baba

Du’a’inmu ya samu ijaba
Ubangiji Ya dubi Baba
Allah ya kara masa muhibba
Mun nemi kariyar Ukuba
Mun nemi tsarin azaba

Salatina ga Annabi mai sahaba
Alfarmar dakin  Ka’aba
Sanya mu daina gaba
Annabi ya yi yarjejniyar Akaba
Allahu ya yi hani da giba

Baba ya yi balaguro
Laulayi ya gangaro
Bokan-Turai ya tunkaro
Allurai aka tsikaro
Jikin Baba ne aka gyaro

Ya yi fama da jinya
Dattijo ya yi hutu
Haurobiyawa na ta surutu
Miyagu na ta kutu-kutu
Murmurewar Baba ce moriya

Ku taho
Ku taho
Mai gani da makaho
A riko sanho
Wasu su dauko baho

Ina dan magori
Mai magani a cikin gari
’Yar mai ganye
Ta zama ’yar gaye
Wai-wai dankari-makari

Ruguntsimin bikin Baba
Dawowarka an samu sawaba
Shinfida tabarmar kaba
Lailaye gidaje da makuba
kawar taryar babba

Marhaba
Marhaba
Maraba
Maraba
Murnar zuwan Baba

Daga birnin
Wato Lantsandan
Mun yi takatsantsan
Wajen tsimayin Baban
Sai ga shi zan-zan

Baban-hurin-huriyya
Ja-gaban wannan jamhuriyya
Dama-damar-kurdin-siyasa
An yi ta sa-in-sa
Damo-da-kura-da-diyya

Usainin-Babajo
Aikinka ya fi na Baba-ojo
Mataimakin Baba Gwarjo
Ka ki  ya yi rawar banjo
Ka fi karfin gwanjo

Babawo
Ka dawo
Ayayo-ayayo
Oyoyo
An yiwo mana awo

Burkin Baburido
Karkarwar kekerido
Shara gudun shorido
Gungurawar kurkurido
Dodon dundumin Dodorido

Wasan wutar kara wowo
Na ga masu kai-kawo
Zo in ba ku kan dawo
Ku kiyayi Babalawo
Magabacin Baba ne ajawo

Masu soki-burutsu
Aura ya yi tutsu
Ku ji da tsuwwar tsuntsu
Kwanyar wasu ta motsu
Kowa ya natsu

Shasha da susu
Jaba da samarin kusu
Da suka wawushe asusu
Yanzu za ku yi bususu
Ta’asarku babu musu

Samirawo
Samar da hatsin tukin tuwo
Samuwar taki na jiwo
Da rahusa za a sawo
Tallafin Jomirawo

Fici da Nanawo
Ga maganin amai da zawo
Ku samu kuzarin kiwo
Ban da yawo
da’a aka ce ku yiwo

Kimanin kwanaki babban lauje da zagaye ana ta yamadidin zagaye-zagayen batun balaguron Baban-burin-huriyya, a lokacin da ya je hutu ya karke da laulayin uwar jiki, duk da cewa ya mika ragamar rikon al’ummar Haurobiya a hannun mataimakinsa, Usainin Babajo. Masu suka-da-burtsatsen maganganu na ta batutuwa marasa kan gado. Kai wasu m a cewa aka yi wai sun tabbatar Baba ba zai komo ba. Koma dai mece ce manufar masu surutu rututu, sai a san cewa ‘jiki da jini, wataran akwai yiwuwar a yi jinya.’ Idan kuwa an jigata, to lallai za a gyagije.
’Yan matan jaba da samarin-kusu sun dauka za su samu sa’ida, wai saboda Baba ya yi balaguro, sai suka ci gaba da bambami, wai a nufinsu gafiya za ta tsira da na bakinta, amma ina! Usainin-Babajo ya yi ta danko su, tamkar Baba na nan. Da suka tabbatar abin babu sauki, sai sukia fara yada jita-jitar cewa Baba ba zai dawo ba. Wasu miyagun kuwa sai suka yi ta sukar lamirin Baba, tare da kwararo yabo ga Usainin-Babajo. Da ganin haka sai fadar Baban-burin-huriyya tya fitar da sanarwa cewa daukacin ayyuka nagargaru da Usainin-Babajo ya aiwatar bayan balaguiron Baba ai sai da ya tuntubi ja-gaban wannan jamhuriyya, shi kuwa ya tabbatar masa da amincewarsa.
A wani bagiren kuwa, shafukan fuskantar bokoko da tukin tuwon-titi da ke mashakatar lilo da tsallake-tsallake sun baza batutuwan kanzon kurege cewa, ‘wai wasu mashahuran mutane na fafutikar ganin sun samu mukamin mataimaki da zarar Usainin -Babajo ya dare bisa karaga, tun da sun samu tabbacin cewa ba lallai ne Baba ya dawo ba. daukacin wadannan  al’amura da aka tsuwurwurta an yi ne da zimmar haifar da rudani a fadin kasar nan. Cikin yardar Mai-duka, Mai-kowa, Mai-komai hakar baragurbi ba ta cimma na-kwadi ba.
Tuni dai Baba ya kama rikon ragama, don haka aikin gama ya gama, mun samu makama, maganin masu karma-karma. Kuma tabbas sai miyagu sun zamato abin kyama; mu dai yi na-damo da karin likimo kafin baragurbi su afka cikin duma, a daidai lokacin da za mu rika damawa, ba tare da damuwa ba.
’Yan makaranatar farfajiyar koyon watsattsake da wangale shafukan wagagen littattafai da mujallu da makalu, ku dabo sayyada, ku dare kekerido da baburido, wasu su tuko shorido-shorido har ma da kurkurido don mu yi ruguntsimin bikin murnar dawowar Baba kasar Haurobiya. Sannan mu himmatu ka’in da na’in wajen yi masa fatan alheri da ba shi kwarin gwiwa don ya ji dadin jan ragama, har ya cimma muradunsa, wadanda suka hada da kalkale kasar nan daga jibgin jibing sharar kwashi–kwaraf da dukiyar al’umma, tare da tabbatar da tsaro, sabanin yadda ake fama da yanayin ‘babu tsaro sai tsoro.’ Baba ka karya lagon masu artabun haramta bobo da kwambon bokoko, amma GARKUWAR GAGARA KUWWA NA SANYA AL’UMMA TSUWWA; GARARUMAR GUMIN GUNDUMAR GUMAMA TA GUNDURIN AL’UMMA; TSOMOMUWAR TSATSUBAR TSUBBACE-TSUBBACE DA TSAFE-TSAFE NA TSOTSE JININ AL’UMMA; FASHI DA MAKAMI, FASHI DA MUkAMI; JIMAMIN JIMURdAR JA-IN-JAR JAMA’A. Uwa -uba dafdalar daular Dala ta damalmala harkokin bunkasa tattalin arzikin Haurobiya. Kodayake dilallan dala, wadanda bas u samu salala ba, sun yi ’yar gala-gala, saboda rashin galala, ballantana a dinka gallaeliyar galila, lallai akwai bukatar a hana masu sulalewa da sulalla.
Barka da zuwa Baban-burin-huriyya! Muna rokon Mai-duka ya ba ka kariya da karfin jagorancin ci gaba da managartan ayyuka da za su kai kasar nan ga gaci, har mu daina tsoron duk wani cici mai jefa wa al’umma firgici.