Bikin bayan sallar azumi da kuma na lahiya
Kusan ko wace shekara kamar yadda yake kasancewa a wasu biranen Kamaru, akwai wani biki na sada zumunci da yake dinga biyo bayan sallar azumi da kuma na lahiya da matasa suke dinga yi izuwa wasu takwarorinsu na wasu birane daban. Ana dinga kiran wannan ziyara na juna da suna “budi” wato kamar dama ce […]
Kusan ko wace shekara kamar yadda yake kasancewa a wasu biranen Kamaru, akwai wani biki na sada zumunci da yake dinga biyo bayan sallar azumi da kuma na lahiya da matasa suke dinga yi izuwa wasu takwarorinsu na wasu birane daban. Ana dinga kiran wannan ziyara na juna da suna “budi” wato kamar dama ce wadannan matasan suke ba kansu wurin ziyarar wasu sassan kasa da basu sani ba. Ana iya cewa ma tankar yawon bude ido ne da a karkashinsa ake shirya wasu gasanni kamar was an kwallo, da su kacici-kacici. Hakan na karkarewa kuma da wasannin gargajiya kamar su kada-kade da kuma raye-raye.
A bana ma an samu irin wannan ziyarar karfafa zumunci a tsakanin juna a birnin Yaounde. Baya ga haka ma a wani matsayi mafi girma masamman tsakanin sarakunan gargajiya, inda wani basaraken kabilar garfawa na yammacin kasa ya kawo wa babban sarkin hausawa na Yaounde ziyara na ban girma inda aka shumfuda wa bakon liyafa da ta dace da matsayinshi. A fadin Basaraken ya kawo wannan ziyara ne domin ya taya ‘yan uwanshi musulmai murnar bikin sallar azumi da suka yi. Ganin cewa ba zai iya kai wa kowa da kowa ziyara ba, a dadlili kenan ya nufi magabacinsu wanda shine sarki Ousmanou Ahmadou Mai Koko domin shi daga nashi bangaren ya isar wa sauran jama’a. Bisa ga dukkan alamu ana iya cewa irin wannan ziyara a wannan lokaci na nuna cewa akwai hadin kai a tsakanin addinai biyu na krista da musulumci. Hakan kuma ya sa kowa da kowa na tafiyar da addininshi ba tare da zangwama ba, wato cikin ‘yanci da kuma walwala.