Bikin biyan-nonon Abzinawa
A ranar ta sili da kofar hanci ga watan Noman-Baba, na shekara ta dubu karamin lauje da sili da kofar hanci, mun ziyarci birnin Tagadas a karo na karamin lauje, inda muka baje na-mujiya don kallo bikin biyan-nonon Auzinawa. Wannan biki ne na gasar kida da rawar auzinawa, wadanda ke zaune a masarautar Tagas da […]
A ranar ta sili da kofar hanci ga watan Noman-Baba, na shekara ta dubu karamin lauje da sili da kofar hanci, mun ziyarci birnin Tagadas a karo na karamin lauje, inda muka baje na-mujiya don kallo bikin biyan-nonon Auzinawa. Wannan biki ne na gasar kida da rawar auzinawa, wadanda ke zaune a masarautar Tagas da kewayenta. Mun ga rikon al’adu na shekara da shekaru, wato iyaye da kakanni.
A ranar bikin Biyan-nono, auzinawa kan kasance da annashuwa da sururi sukan girka kayan dundume kururu, wadanda suka hada da cukubus da algaragis da alkubus. Mu dai mun bude tumbinmu mun cunkusa masa naman tanderu.
Auzinawan Tagas mutane ne masu karamci, domin har kiranmu suka rika yi kan lallai mu zo mu dundume kururu. Kuma ko’ina muka kewaya sai mu ga kowa na shagalinsa. Kusan ko ina mutum ya gitta sai yaga dimbin al’umma na ta kwararowa, babu mai jin na wani.
Ni dai na ga doguwar dabba; nag a tarin yashin Hamada. Hakika na zaune bai ga gari ba, kamar yadda masu ayren hau-hau wajen hawan sa ba tare das a-in-sa ba, suka furta.
A matsayina na Direban Allin wannan farfajiya na cika ban mamaki jin cewa an yi gasa tsakanin Gabasawa da Yammatawa, kuma har aka ce wai Gabasawa sun lashe gasa, to wai wane nee alkalin gasa? Ta yaya aka fasko cewa Yammatawa sun ci kasa a wannan gasar cashewa ta Biyan-nono?
Hakika wadannan tambayoyi da na bijiro da su ina ganin wajibi ne ga Sardaunan Abzin, tunda shi a kasar Haurobiya yake, ya yi yunkurin bijiro da su ga masu shirya bikin biyan-nonon Abzinawa, ta yadda idan suka bayar da cikakkiyar amsa kowa zai gamsu.
Ni dai a wannan ziyara ta karamin lauje da na kai kasar Abzin, na tabbatar da na zama babban bako wato dai ni ne:
Bakon Mata Meye da Taketa da Damagaran, saura kadan in zama gangaran, sai na arce zuwa Tagadas, daga nan na zarce zuwa birnin Arlit. Wannan birni na Arlit birnin ne mai ruwan kauye. Domin akwai kayan more rayuwa wadanda suka yi daidai da na manyan kasashen duniya, sannan akwai bukkokin talakawa wadanda ke fama da talalar talauci a gefe da gefe.
Birnin Arlit da Ciro da Tumfadak duk suna karkashin masarautar Abzin, Haurobiyawan da suka ziyarci wadannan garuruwa hakika sun gamsu da yadda Abzinawa ke rikon al’adunsu.
Sakon direban alli
A madadin masu koyon watsattsake da buda wagagen litattafai na wannan farfajiya, ina taya dan makarantarmu Malam Yahaya, murnar turkeshi da za a yi a turken rayuwa a ranar Sili ga watan Dashen-Baba, a Unguwar Masu kewaya kyalle da ibada da ke birnin Dabo. Wadanda ba su samu halarta ba kuwa suna iya tuntubarsa a kurtun maganarsa, mai lambobi kamar haka: zagaye da madambaci da manuniyar sama da karamin lauje da madambaci da sili da manuniyar sama da zagaye da sili.