Bikin cika shekara 20 da kafa kamfanin Daily Trust ya gudana a Abuja

A jiya Alhamis ce Kamfanin Media Trust, mai buga jaridun Daily Trust da Aminiya ya yi bikin cika shekara 20 da kafuwa, inda masana harkokin watsa labarai suka yi waiwaye tare da fashin baki kan nasarori da kalubalen da ke fuskantar aikin jarida a yau. A yayin taron wanda aka gudanar a Abuja, daya daga […]

Bikin cika shekara 20 da kafa kamfanin Daily Trust ya gudana a Abuja

A jiya Alhamis ce Kamfanin Media Trust, mai buga jaridun Daily Trust da Aminiya ya yi bikin cika shekara 20 da kafuwa, inda masana harkokin watsa labarai suka yi waiwaye tare da fashin baki kan nasarori da kalubalen da ke fuskantar aikin jarida a yau.

A yayin taron wanda aka gudanar a Abuja, daya daga cikin daraktocin kamfanin, Alhaji Rabi’u Garba ya  ce gaskiya da jajircewa da kwatanta adalci ne sirrin nasarar da jaridar ta samu a tsawon wadannan shekaru. Ya ce jaridar ba kawai a Najeriya ba, ta zama a sahun gaba a Afirka baki daya. 

Ya ce, “Muna godiya ga dukan wadanda suka halarci wannan taro don taya mu bikin cika shekara 20 da kafuwa. Hakika mun samu taimakon Ubangiji har muka kai ga samun nasara. Kodayake wasu jaridu da dama da muka fara tare ko suka rigaye mu, tuni sun durkushe a wannan bulaguro mai cike da kalubale, amma cikin yardar Allah muna nan, ba kawai muna nan ba, a’a, ci gaba muke kara samu a kullum.”

“Zan iya cewa mun sha bamban da sauran, domin wasu jaridun an kafu su ne da kudade masu yawan gaske, amma mu mun fara ne da kadan, kuma da kadan din ne muka dore har zuwa yau. Mun fara da gidan haya daga Kaduna, amma sannu a hankali mun mallaki  ofishi na biliyoyin Naira a nan Abuja,” inji shi.  

Shugaban taron kuma tsohon shugaban Kamfanin Jaridun Punch, Cif Ajibola Ogunsola ya bayyana cewa jaridun Daily Trust sun cancanci yabo bisa namijin kokarinsu wajen wayar da kan al’ummar kasar nan ta fuskoki daban-daban ba tare da nuna bangaranci ko kabilanci ko addini ba. Ya bukaci jaridun su kara ninka kokarin da suke yi a tsawon shekara 20 da suk shafe suna tsage gaskiya komai dacinta.

Taron mai taken “Aikin Jarida A Matsayin Kasuwanci: Labarai, Ra’ayoyi da Tallace-Tallace,” ya samu sanya albarka daga fitattu kuma zakakuran jami’an watsa labarai da suka hada da Mawallafin Jaridar Business Day, Frank Aigbogun da Shugabar Gidan Rediyon Hot FM, Sanata Chris Anyanwu da Babban Daraktan MediaReach, Tolu Ogunkoya da Shugaban Jaridar Intanet ta Premium Times, Dapo Olorunyomi da suka tattauna a kan maudu’in, yayin da fitacciyar ’yar jaridar nan Kadaria Ahmed ta kasance mai shiga tsakani.

Haka kuma an karrama wadansu daga cikin tsofaffin ma’aikata da shugabannin gidan jaridar da suka hada da Alhaji Isiak Ajibola da Alhaji Rabi’u Garba da Ishak Modibbo Kawu da sauransu. Kuma taron ya samu halartar manyan baki da kwararrun ’yan jarida irin su tsohon Manajan Daraktan Kamfanin NAN, Malam Wada Maida da Mai Taimaka wa Shugaban kasa kan HarkokinWatsa Labarai, Malam Garba Shehu da tsohon Ministan Abuja Aliyu Modibbo da Hakeem Baba Ahmed da tsohon Editan Daily Trust kuma Shugaban Hukumar NBC, Modibbo Kawu da sauransu.