Bikin cikar Najeriya shekara 59 da samun ’yanci
Fatar alheri a gare ku amintacciyarmu jaridarmu mai albarka. Don Allah Edita, ka taimaka mini ka ba ni dama kamar yadda aka saba, domin in yi tsokaci game da bukukuwan cikar Najeriya shekara 59 da samun ’yancin kai. Tabbas abin takaici ne a ce shekara 59 da samun ’yancin kai, amma babu wani abin yabawa […]
Fatar alheri a gare ku amintacciyarmu jaridarmu mai albarka. Don Allah Edita, ka taimaka mini ka ba ni dama kamar yadda aka saba, domin in yi tsokaci game da bukukuwan cikar Najeriya shekara 59 da samun ’yancin kai. Tabbas abin takaici ne a ce shekara 59 da samun ’yancin kai, amma babu wani abin yabawa da dan Najeriya zai yi alfahari da shi, face lalacewar shugabanci da tsintar kai cikin halin kunci da talauci da talakan Najeriya ke fama da shi a halin yanzu. Kasa babu wutar lantarki, ba hanyoyi, matasa babu ilimi, ga uwa uba alfarma da ta dabaibaye gwamnatocinmu. Ga kuma cin hanci da rashawa da ya dade da samun wurin zama a Najeriya, Allah Sarki talakan Najeriya! Ya Allah Ka sanya tausayi a zukatan shugabanni da wakilanmu. Ka kuma taimaki kasarmu Najeriya, amin.
Daga Murtala Ahmed Abubakar Kwalli Gidan Doki. Kano 07068295953.
Ranar Yaki da Cin Zarafin Mata
Assalamu alaikum Edita. Zan so in yi tsokaci a kan Ranar Yaki da Cin Zarafin Mata da Majalisar Dinkin Duniya ta ware. To a gaskiya mu dama can tun tale-tale addininmu na Musulunci ya yi tanadin hakan, sannan kuma muna kwatantawa daidai gwargwadon iko.
Daga Mansur Sule Hadeja, 08066004696.
Hukuncin kalaman nuna kiyayaya
Hukuncin kisa kan maganar nuna kiyayya bai dace ba. Abin da ya kamata shi ne a daure mutum na tsawon lokaci don hukunta masu yin kalaman nuna kiyayaya.Hakan zai magance yawan tashin hankali da kashe-kashe da kalaman nuna kiyayya ke haifarwa.
Daga Muhammed Sani Aliyu
Nasarar Gwamna Masari a kotu nasara ce ga Jihar Katsina
Hakika nasarar da Gwamna Aminu Bello Masari, ya samu a Kotun Daukaka Kara da dan takarar Gwamnan Jihar Katsina a Jam’iyyar PDP, Yakubu Lado ya kai nasara ce ga al’ummar Jihar Katsina da ci gaban dimokuradiyyar jihar, ganin cancanta da sanin ya kamata da son ci gaban jihar Gwamna Masari ya sa gaba. Muna murna da fatar Allah Ya taya shi riko Ya ba shi ikon sauke wannan nauyi na al’ummar Jihar Katsina, amin.
Daga Usman Manika Mairuwa Road Funtuwa 08060309856.
Gyaran hanya Doko zuwa Ringim
Assalamu alaikum, mu al’ummar garin Doko ba za mu gajiya ba wajen tuna wa Mai girma Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Badaru Abubakar Talamiz alkawarin da ya yi mana na shimfida mana kwalta daga garinmu na Doko zuwa garin Ringim, wanda hakan zai taimaka wa al’ummar yankin da kewaye ta fuskar kasuwanci da sufuri. Daga karshe muna fata Allah Ya sa kiranmu ya isa ga kunnuwan da suka dace
Daga Mutawakkil Gambo Doko, Karamar Hukumar Garki, Jihar Jigawa. 07032695589
Taya murnar ga Gwamna Ganduje
Assalam alaikum. Ina taya murna ga Dokta Abdullahi Umar Ganduje bisa nasarar da Kotun Daukaka Kara ta tabbatar masa. Da fatar zai ci gaba da gudanar da mulkin adalci a Jihar Kano, ba tare da nuna bambancin siyasa ba. Sannan ina kira ga Abba Kabir Yusuf, na Jam’iyyar PDP a kan ya rungumi kaddara ya mayar da komai ga Allah, Allah zai kawo masa mafita. In da rai da rabo kuma Hausawa sun ce gobe ma rana ce!
Daga Ali Abdullahi Doron Baga, Jihar Borno
Jinjina ga Shugaba Buhari
Assalam Edita. Ina jinjina wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a kan rufe iyakokin kasa, domin da haka kasarmu za ta ci gaba. Mu duba mu ga kasashen waje kamfanoni nawa gare su a Najeriya, bayan kayansu da ake shigo da su, to amma Najeriya kamfani nawa gare ta a kasashen waje? Duk kasar da ta ci gaba to sai da ta shiga cikin matsi ’yan uwana ’yan Najeriya sai mun yi hakuri. Allah Ka ba Buhari ikon ci gaba da ayyukan alheri ga kasa.
Daga Sufiyanu Aliyu Addam Yabo Sakkwato, 08161788025.
Shawara ga Shugaba Buhari
Assalam Aminiya. Ina son ku ba ni dama domin bai wa Shugaba Muhammadu Buhari shawara. Ina gani babu hikima ko dabara wajen rufe iyaka da aka yi domin a yanzu talaka yana cikin wani hali mai wahala a yanzu ta kai har gona ake zuwa ake sayen shinkafar talaka. Da kaka an sayi kwanon shinkafa Naira 850 zuwa Naira 900 don Allah shugaba Muhammadu Buhari ka share wa talakawanka hawaye.
Daga Yakubu Rabi’u Takai 08091473719.
Ta’aziyya ga Masarautar Nasarawa
Muna mika ta’aziyya ga ma’aikatan FCDA da ’yan uwa da abokan arzikin Alhaji Umar Yusuf Sodangi, Jakadan Nasarawa kuma aminin Mai martaba Sarkin Nasarawa. Jihar Nasarawa da Najeriya mun yi rashin gwarzo, dan kasa mai kishin zuci da tausayin jama’a da yawan alheri. Allah Ka jikan Darakta a FCDA, Alhaji Umar Yusuf Sodangi. Allah Ya yi masa rahama Ya kai haske da ni’ima cikin kabarinsa. Allah Ya bada hakurin rashinsa, amin.
DagaYusuf Kangiwa (YCK) 08069448014.
Jinjina ga Gwamnan Zamfara
Assalam Editan Aminiya mai farin jini. Ka ba ni dama in yi jinjina ga Gwamnanmu, Dokta Bello Matawalle bisa hikimar da Allah Ya ba shi ta yin sulhu da masu garkuwa da mutane. Mu talakawa sai murna domin a da duk inda za mu bi abin fargaba ne. Da fatar Allah Ya yi masa jagora, amin.
Daga Tajudeen Kwazo Kauran Namoda 08174569088.
Ga Gidauniyar Kwankwasiya
Salam Editan Aminiya. Don Allah ka mika mini addu’ata ga yaran da Gidauniyar Kwankwasiyya ta biya wa karatu. Ya Allah Ka sa za su fara a sa’a! Ya Allah Ka sa yadda aka taimake su su taimaki na kasa da su.
Daga Baffa Garkuwan Hasken Dala
Akwai gyara a aikin jami’an Kwastam
Aminiya mai dubun albarka da fatar kuna lafiya. Ina so ku isar min da sakona cewa gaskiya ba na ji dadi kan yadda jami’an Kwastam suke gudanar da aikinsu. Har shaguna suke fasawa don kwace shinkafa me ya sa lokacin da ake shigo dai ita, ba su kama wani ba lokacin da ba a rufe boda ba. Allah Ya sa mu gama lafiya.
Daga Ali Bismak Moto Legas, 09069158247.
Kira ga Baba Buhari
Ya mai girma Shugaban Kasa, ka sani fa kai dan Arewa ne kuma na tabbata ka fi ni sanin haka. To amma wallahi wannan yankin namu ya fi kowane yanki shan wahala a lokacin mulkinka, Shi ne koma baya a fannin tsaro da tattalin arziki da ilimi da harkar lafiya da zamantakewa da ayyukan raya kasa. Ka sani kowa ya hau wannan mulki yana fara duba nasa yankin ne kafin na wasu kai da jami’an gwamnatinka sai dai ku duba na wadansu kun bar naku, to in ba ku yi yanzu ba yaushe za ku yi?
Daga Ahmad Muhammad Wamakko 07068039968.
2023: Sai Sanata Kwankwaso
Assalam Edita. Ka mika min gaisuwata da godiyata ga ’ya’yan Jam’iyyar PDP na Jihar Kano da Mai girma Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso. Tabbas muna yi muku godiya game da nasarar da jam’iyarmu ta APC ta samu a lokacin zaben Shugaban Kasa na 2019 a Kano. Ya Mai girma Sanata da yardar Allah sai ka yi Shugaban Kasa a 2023. Kai za mu bi mai kishin talakawa. Allah Ya kai mu 2023 lafiya.
Daga Maikudi Ibrahim Zeze, Lungun Mabuga Warure Kano, Mazaunin Ajegunle Legas. 09025253392, 08186211072
Gaskiya ne Buba Galadima
Da farko ina jinjina maka wajen fadar gaskiya komai daci kuma ba ka tsoro ba ka shakka don haka yanzu mu gane wanda muka zaba. Dama an ce kowa ya sayi rariya ya san sai ta zubar da ruwa.
Daga Dan Bukur Yaro, 08162565182
Kira ga Kungiyar Kwadago
Assalamu alaikum Editan Aminiya, jaridarmu mai farin jini. Don Allah ka mika sakona zuwa ga Kungiyar Kwadago a kan me ya sa duk lokacin da suke son a fara yajin aiki su bari sai tsakiyar wata ko wata ya kusan karewa ? To ina son in fada musu wannan yana sa ma’aikata cikin wahala kafin su samu kudinsu na wata. Idan har za a fara, to a rika farawa farkon wata lokacin kowa ya rika. Don Allah a kula.
Daga Umar A. Mohammed Gusau (NAMU-NAMU) 08081167862.
Gaskiya muna jin jiki
Assalam Edita, barka da fama. Don Allah ka ba ni dama cikin wannan jarida mai albarka, don in yi kira ga Shugaba Buhari ya yi wa Allah ya duba matsalolin talakawa domin ciyawar da ke cikin ruwa ba ta san ana zafi ba. Mu dai mun kasa sanin halin da muke ciki.
Daga Sulaiman Dan Jarida Gusau. 08068854869
Jinjina ga Shugaban Majalisar Jihar Kaduna
Assalamu alaikum Edita. Ina son ka ba ni dama in yi jinjina ga Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Alhaji Aminu Abdullahi Shagali a kan ayyukan da yake na alheri. Ina fata Allah ya biya masa bukatunsa a shekarar 2023.
Daga Salisu Yunusa. 0706312585, 09072028843.
Taya murna ga gwamnonin Kano da Filato
Salam Edita. Ina taya Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje da Gwamnan Jihar Filato Barista Simon Bako Lalong game da nasarar da suka samu a Kotun Daukaka Kara kan zabensu. Lallai wadannan alkalai sun yi adalci . Allah Ya yi wa gwamnonin biyu jagora zuwa ga nasara, amin.
Daga Aliyu Korau Bajari, Gishirin Hassan, Karamar Hukumar Ibbi Jihar Taraba, 07013322949