Bikin dodannin Legas: Basarake ya buƙaci mata su killace

Za a yi bikin doddanin a yankin Ikorodu da ke Jihar Legas.

Bikin dodannin Legas: Basarake ya buƙaci mata su killace

A ci gaban da shirye-shiryen bikin doddani da za a yi a yankin Ikorodu a Jihar Legas, babban basaraken yankin ya buƙaci mata su killace kansu a cikin gida a lokacin bikin wanda aka shirya za a gudanar a ranar 16 ga watan Mayun nan.

Basaraken Ayangburen na Masarautar Ikorodu, Oba Kabiru Adewale Shotobi, ya gargaɗi mata su guji kai-komo a cikin garin lokacin bikin.

A wata wasiƙa ɗauke da kwanan wata 16 ga watan Afrilun 2024 da aka aike wa da Daraktan Lafiya na Babban Asibitin Ikorodu, Sarkin ya shawarci mata ma’aikata a asibintin su kasance a gidajensu.

Wasiƙar tana da taken ‘Sanarwar Magbo (Oro) ko kuma Bikin Doddani na Oro na shekarar 2024’.

Basarake Shotobi, ya ce bin al’adar bikin shi ne mata su kasance a gidajensu, ya kuma shaida wa Daraktan Likitocin cewa Babban Asibitin Ikorodu yana cikin yankin gargajiya na Oro.

“Wannan shi ne dalilin sanar da ku bikin wanda aka shirya a ranar Alhamis 16 ga Mayun 2024, bisa ga al’adar an shawarci dukkan mata da su kasance a gidajensu kuma su guji yin kai-komo cikin gari yayin bikin na Oro.

“Don Allah mun lura cewa wajen aikinku ya faɗo cikin yankin da za mu gudanar da bikin gargajiya na Oro, don haka muka shawarce ku da ku bi al’adar gari.

“Za a yaba da haɗin kanku don samun nasarar bikin. Na gode muku. Allah Ya saka da alheri,” in ji Sarkin.

Bikin Doddani na Oro wani biki ne na gargajiya na shekara-shekara da maza ke yi a ƙasar Yarbawa. A matsayin biki mai muhimmanci, ana amfani da shi don faranta wa gumakan bautarsu rai da neman zaman lafiya da tsaro a ƙasar Yarbawa.