Bikin Gasar Sarauniyar Kyau Musulma ta Duniya ya jawo cece-kuce
Bikin gasar sarauniyar kyau Musulma ta duniya da aka gudanar a Indonesiya makon jiya ya jawo cece-kuce.kasashe biyar ne suka shiga gasar da suka hada da Najeriya da Bangladesh da Malaysia da Iran da Brunei da kuma mai masaukin baki Indonesiya.A yayin bikin ‘yan matan da suka fafata sun yi shigar da ba ta fitar […]

Bikin gasar sarauniyar kyau Musulma ta duniya da aka gudanar a Indonesiya makon jiya ya jawo cece-kuce.
kasashe biyar ne suka shiga gasar da suka hada da Najeriya da Bangladesh da Malaysia da Iran da Brunei da kuma mai masaukin baki Indonesiya.
A yayin bikin ‘yan matan da suka fafata sun yi shigar da ba ta fitar da tsiraici ba inda suka rika tafiyar mage a gaban dubban ’yan kallo. Daga baya aka sanar da ‘yar Najeriya Obabiyi A’ishah Ajibola ce ta lashe gasar.
A lokacin da aka bayyana A’ishah ce ta lashe gasar sai ta yi sujuda sauran matan da suka fafata suka taya ta murna.
“Na gode wa Allah da Ya ba ni nasara kuma wannan zai nuna wa jama’a Musulunci yana da kyawu.” Inji A’ishah ‘yar shekara 21.
Eka Shanti ce ta kirkiro bikin shekaru uku da suka wuce bayan ta rasa aikinta na jarida a dalilin ta sanya hijabi.
Sai dai al’amarin ya jawo cece-kuce, inda Sheikh Isa Adeeyo daga Najeriya ya ce, “Wannan harumun ne, babu shi a cikin Musulunci.”
Abu Zainab shahararren malami dan Najeriya mazaunin Birtaniya ya ce Manzon Allah SAW ya hana mu kwaikwayon Yahudu da Nasara, kuma duk wanda ya kwaikwayi wadansu mutane to zai tashi a cikinsu.
Daraktan kungiyar Kare Hakkin Mata Musulmi (MURIC) Farfesa Ishak Akintola ya taya A’ishah murnar nasarar da ta samu, inda ya ce ba a nuna tsiraici a bikin ba, ko wani abu da ya saba wa shari’a ba. Baya ga haka, an gwada wadanda suka wajen karatun al’kur’ani da tarihin Musulunci da hukunce-hukuncen Musulunci da sauransu.