Bikin gasar sarauniyar kyau ta duniya ya samu cikas

Bikin gasar sarauniyar kyau ta duniya karo na 63 da aka shirya gudanarwa a Indonesiya ya samu cikas, inda daruruwan Musulmin kasar suka yi alla-wadai da shi ta hanyar gudanar da zanga-zanga.Da farko an shirya fadar sakamakon wacce ta lashe kambin sarauniyar kyau ta duniya a dakin taro na Sentul International Conbention Center da ke […]

Bikin gasar sarauniyar kyau ta duniya ya samu cikas

Matan da suka fafata don neman sarauniyar kyau sanye da tufafin IndonesiyaBikin gasar sarauniyar kyau ta duniya karo na 63 da aka shirya gudanarwa a Indonesiya ya samu cikas, inda daruruwan Musulmin kasar suka yi alla-wadai da shi ta hanyar gudanar da zanga-zanga.
Da farko an shirya fadar sakamakon wacce ta lashe kambin sarauniyar kyau ta duniya a dakin taro na Sentul International Conbention Center da ke Jakarta babban birnin kasar a ranar 28 ga watan Satumba, amma bayan zanga-zangar sai aka mayar da bikin birnin Bali daya daga cikin manyan garuruwan kasar marasa tsattsauran ra’ayin addini.
An fara gudanar da bikin ne a ranar 8 ga watan Satumba inda matan da za su fafata 130 suka yi shigar kasar Indonesiya mai suna Nusantara, sannan suka yi tafiyar mage.
Yayin bikin an gudanar da kade-kade da raye-raye da kuma wake-waken kasar Indonesiya.
Sai dai ko bayan an mayar da shi Bali an ci gaba da gudanar da zanga-zanga, inda wadanda suka shirya bikin suka ce zai yi matukar wahala a ci gaba da bikin a Bali, inda kuma ake kokarin mayar da shi Jaba.
A yanzu an fara rade-radin za a mayar da shi yankin da kabilar Hindu suke da rinjaye a kasar.
“Al’amarin ya cukurkude, ban kuma yi tsammanin bikin zai samu nasara a Bali ba.” Inji Nana Putra, Babbar Daraktar shirye-shirye da watsa biki ta kafafen sadarwa ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFC.
Masu zanga-zangar alla-wadai da gasar sarauniyar kyau a IndonesiyaA yanzu dai babu tabbacin takamaiman wurin da za a sanar da sakamakon karshe a ranar 28 ga watan Satumba.