Bikin kaddamar da Nagarta Cikin Aminci: Ranar da M. D. Yusuf ya sha yabo

A ranar Larabar makon jiya ce aka gudanar da bikin kaddamar da littafin ‘Nagarta Cikin Aminci,’ littafin da yake kunshe da tarihin tsohon Sufeto-Janar Muhammad Dikko Yusuf.Bikin, wanda ya hada da kaddamar da gidauniyar tara kudi domin gina katafariyar Cibiyar Bunkasa Ilimi Ta M. D. Yusuf ya gudana ne a babban zauren taro na Gidan […]

Bikin kaddamar da Nagarta Cikin Aminci: Ranar da M. D. Yusuf ya sha yabo

Tsohon Shugaban Kasa, Janar Yakubu Gowon, yana jawabi a zauren taron kaddamar da littafin M. D. Yusuf, a hagunsa, Gwamnan Jihar Kaduna ne, Alhaji Mukhtar Ramalan YeroA ranar Larabar makon jiya ce aka gudanar da bikin kaddamar da littafin ‘Nagarta Cikin Aminci,’ littafin da yake kunshe da tarihin tsohon Sufeto-Janar Muhammad Dikko Yusuf.
Bikin, wanda ya hada da kaddamar da gidauniyar tara kudi domin gina katafariyar Cibiyar Bunkasa Ilimi Ta M. D. Yusuf ya gudana ne a babban zauren taro na Gidan Arewa da ke Kaduna, inda al’umma maza da mata suka halarta.
Taron ya fara gudana ne bayan budewa da addu’a, inda daga bisani Shugaban Kwamitin kaddamarwa, Alhaji Ibrahim A. Coomassie ya gabatar da jawabin maraba. A yayin da yake wa mahalarta taron maraba, ya kuma yi amfani da wannan dama, ya nuna muhimmancin bikin da kuma mutumin da ake bikin dominsa.
“Mun taru ne nan domin bikin karrama muhimmin mutum, jigon gina al’umma, wanda babu ruwansa da nuna kabilanci. Ya kasance jagora mai kwato ’yancin talakawa, mai gaskiya da amana, wato Alhaji M. D. Yusuf.”
A matsayinsa na Shugaban Taro, tsohon Shugaban kasa, Janar Yakubu Gowon, a nasa jawabin, shi ma yaba wa M. D. Yusuf ya yi, inda ya fassara shi da mutum mai kishi da kaunar talakawa. Ya ce tun a 1966 ya fara haduwa da shi a Legas, inda daga bisani ya ci gaba da mu’amala da shi, a matsayinsa na Shugaban kasa.
Farfesa dahiru Yahaya, shi ne Babban Bako Mai Jawabi. A matsayinsa na kwararren malamin jami’a, ya gabatar da dogon jawabi da Ingilishi mai taken ‘Succession in Nigerian Political Culture: The Role of Two Cities and the Third.’
Jawabin nasa dai ya yi ta yunkuri yana tumbatsa ne cikin nazari, tariya da sharhi game da al’amuran siyasa da mulki a Najeriya, kamar kuma yadda ya yi ta alakanta al’amuran da garuruwan Katsina da Zariya da Kano; kamar yadda suka shafi tarihi da rayuwar M. D. Yusuf.
A jawabin nasa ne ya canja wa dimokradiyya ma’ana, musamman lokacin da ya danganta ta da Najeriya. Kamar yadda ya ce: “Ba kamar yadda aka sani ba, cewa ma’anar dimokradiyya ita ce, mai yawa shi ke da mulki, amma ba a Najeriya ba, domin kuwa a nan kasar, dimokradiyya al’amari ne da ya shafi ra’ayi, karfin zuciya da kuma hikima.”
A yayin da yake kara bayani game da wannan sabuwar ma’ana ta dimokradiyya, Farfesan ya kawo labarai da misalai game da muhimman ’yan siyasa kamar Janar Buhari da sauransu. Kamar yadda ya ce, wani hamshakin mutum ya tambaye shi cewa, mene ne dalilin da ya sanya Janar Buhari bai zama Shugaban kasa ba, duk kuwa da cewa an yi imanin cewa yana cin zabe? Shi ne ya amsa masa da cewa, saboda a Najeriya, ana zartar da sunan mutumin da za a ba shugabanci ne tun ma kafin a tafi fagen zabe. Yana nufin cewa akwai wasu kungiyoyi na fitattun al’umma, da su ke juya akalar al’amuran siyasar Najeriya. Idan suka ga dama suka ce wane zai zama Shugaban kasa, shi ke nan.
Ba nan jawabin nasa ya tsaya ba, domin kuwa sai da ya ci gaba da tabo al’amura masu yawa da suka shafi ’yan siyasa da kuma yanayin siyasar kasar nan. Misali, ya kawo batun Janar Olusegun Obasanjo, sannan kuma ya yi bayanin dalilin da ya sanya har ya samu amsuwa kuma ake kaunarsa a Arewacin Najeriya.
Kamar yadda ya ce: “Daga dukkan yadda al’amura suke gudana kuma duk ta ida ka kalla, Janar Obasano dai ya kasance dan lelen Arewa. Babban dalilin da ya sa ya samu amsuwa kuma ake kaunarsa a Arewa shi ne, saboda halinsa na zumunta, kamar yadda aka san Yarabawa na ainahi da ita. Shi ya kasance mutum wanda bai damu da nuna kabilanci ba, ga shi kuma mai amincewa da mutane.”
Wani muhimmin batu da Farfesan ya tabo a jawabinsa, shi ne na batun hadin kan Najeriya, inda ya bayyana mutum na farko da ya fara hada kan garuruwa da kabilu mabambanta zuwa shiyya daya, bisa kan tsarin mulki daya. Kamar yadda ya ce, mutumin da ya fara samun nasarar yin haka na farko a Najeriya, shi ne Shaikh Usman danfodiyo, domin kuwa shi ne mutumin da ya hada yankin Arewa da Middle Belt (Arewa Ta Tsakiya) suka zama yanki daya, wato Arewa kawai. Ke nan ya hada wasu yankuna na Nufawa da Yarabawa zuwa cikin khalifancinsa, shekaru 200 da suka gabata. Shi ne ya share wa Turawa hanya a irin wannan salon, inda shekaru 100 da yin nasa hadin-gambizar, su kuma suka zo suka hada Arewaci da Kudancin Najeriya, suka samar da kasa daya, wacce a yau ake kiran ta da sunan Najeriya.
Masanin tarihin, a lokacin da ya zo bayani game da Muhammad Dikko Yusuf, wanda a kan littafin tarihinsa ne aka taru, sai ya bayyana shi a matsayin dan Katsina ta haihuwa, dan Kano ta hanyar zama. Ma’ana, yana nufin tsohon Sufeto-Janar din ya kasance mai gari biyu, Katsina da Kano. Ya kuma bayyana shi a matsayin babban jigo a siyasar Najeriya, wanda ya taimaka sosai wajen tafiyar da mulkinta da gudanar da al’amuranta.
Baya ga M. D. Yusuf, Farfesa dahiru Yahaya ya yi bayani sosai game da gudunmowar Sarakunan Gargajiya na dauri, musamman ma dai na Katsina, Muhammad Dikko (kakan M. D. Yusuf) da kuma Sarkin Kano, Alhaji Abdullahi Bayero.
Shi kuwa Farfesa Abdalla Uba Adamu, a matsayinsa na mai sharhi kan littafin ‘Nagarta Cikin Aminci’ a wurin taron, ya bude sharhin nasa ne da yabo tare da gwarzanta M. D Yusuf. Kamar yadda ya ce: “Alhaji Muhammad Dikko Yusuf mutum ne da ya kasance mai tsattsauran ra’ayin siyasa, mai ilimi, kamar kuma yadda ya kasance mai yi wa addininsa hidima, haka kuma mai tallafa wa matasa. Duk wata harka da ya tsoma hannunsa a cikinta, yakan inganta ta, ya karfafa ta. Yana da wahala a samu wani dattijo a Arewacin Najeriya da ya jajirce, ya sama wa kansa daraja da martaba a tarihi a cikin ruwan sanyi, ba tare da caragadai da cakwaikwaiwar kafafen watsa labarai ba, sannan kuma har ya zama ya samu sanayya da yabawa, wadanda za su dore a bayan rayuwarsa kamar M. D. Yusuf.”
A sharhinsa, Farfesan ya yi tattaki ne cikin rayuwar M. D. Yusuf, kamar yadda aka zayyana a littattafai biyu, ‘The Aristocratic Rebel’ na Ayo Opadokun da kuma ‘Nagarta Cikin Aminci’ na Abubakar Mijinyawa.
Da aka zo batun kaddamar da littafin da kuma gidauniyar gina Cibiyar Bunkasa Ilimi Ta M. D Yusuf, a nan ma an samu gudunmowar da ta kai Naira miliyan talatin. Babban Mai kaddamarwa, Alhaji dahiru Barau Mangal ne ya ba da gudunmowa mafi tsoka ta Naira miliyan biyar. Jihohin Katsina da Kaduna ne suka take masa baya da Naira miliyan biyu-biyu kowaccensu.
An dai tashi taron lafiya.